Connect with us

News

Ƴan ISWAP sun rabawa matafiya tsoffin takardun Naira

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake zargin ‘yan kungiyar ƴan ta’adda na ISWAP ne sun raba makudan kudade na tsofaffin takardun naira ga matafiya da dama a gaɓar tafkin Chadi.

 

Advertisement

A cewar rahoton Daily Trust, lamarin ya faru ne bayan kauyen Mairari da ke kan hanyar Maiduguri/Monguno a ranar Asabar a karamar hukumar Guzamala ta jihar Borno.

Eriksen Zai Yi Jinyar Wata Uku Zuwa Hudu

Wata majiya a Maiduguri ta shaida wa jaridar cewa ƴan kungiyar ta ISWAP na sanye da kakin soji su na tuka motoci masu ɗauke da bindigu guda biyu.

Advertisement

 

Wani mazaunin garin mai suna Bakura Ibrahim ya ce maharan sun zauna a karkashin wata bishiya, inda su ka tsaya a gefen titi dauke da jakunkunan tsofaffin takardun kudi na naira.

Advertisement

 

“Mun bar Monguno da misalin karfe 12 na rana. Da muka tunkari Mairari, babu shingayen binciken ababen hawa a yankin sai mu ka firgita.

Advertisement

 

“Sai su ka tsayar da mu su ka tambaye mu ko za Maiduguri za mu je, sai su ka fara ba kowane mutum takardar tsohon naira, har na Naira dubu 100 kowannen mu. Sai abin ya bamu matukar mamaki. Sun baiwa kowane a cikin motar da mu ke ciki ta Golf Volkswagen,” in ji Bakura.

Advertisement

 

Wata majiya ta kara da cewa, “Kungiyar ta ce mana kawai, “Idan kuna tunanin za ku iya zuwa bankuna ku canza ta zuwa sabuwar Naira, ku je ku yi; Allah Ya sa shi amfane ku.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending