Connect with us

News

Kotu Ta Bayar Da Belin Alkalan  Kotunan Shari’ar Addinin Musilinci

Published

on

DAGA MARYAM JAMILU BABA

Wata kotun majistiri dake zamanata a unguwar gyadi-gyadi Kano ta bayar da belin wasu Alkalai da kuma ma’aikatan kotun shari’ar addinin musulinci da ake tuhuma da batan kudi sama da naira miliyan 500 na marayu.

Advertisement

A zaman kotun na wannan rana lauyan hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa na jahar Kano Barista Zaharaddin Kofar mata ya bayyana wa kotun cewa, rana ce da aka sanya domin jin nazarin kotu akan rokon da lauyoyin wadanda ake tuhuma suka yi na bada belinsu.

Dan Wasan Tsakiyar Chelsea Jorginho Ya Koma Arsenal

Ana  tuhuma ta farko ana zargin mutane 15 da yin sama da fadi da naira miliyan 96.
Mutanen sun hada da Hadi Tijjani Ma’azu, Bashir Kurawa, Basiru Baffa, Husaina Imam, Yusuf Abdullahi, Alkasim Abdullahi, Jafar Ahmad, Adamu Balarabe, Aminu Abdulkadir, Abdullahi S. Zango, Garba Yusuf, Mustapha Bala Ibrahim da dai sauransu.

Advertisement

Bayan haka ne aka sake gabatar da wasu mutane biyar da suka hada da Bashir Kurawa, Sa’adu Umar, Abdullahi Tijjani , Maryam Jibrin, Usaina Imam da ake zargi da batan kudi naira miliyan 408.

Bayan dogon nazari da Alkalin kotun mai shari’a Mustapha Sa’ad Datti ya yi ne, ya bayar da belin mutanen da ake zargi tare da gindaya mu su sharuda kafin su shaki iskar yanci.

Advertisement

A sharadin belin kunshin tuhuma ta farko mai shari’ar ya gindaya mu su sharadin kawo mutane biyu kowannensu , mutum na farko zai ajiye naira dubu 200 sai kuma mutum na biyu zai ajiye takddun gidansa ko fili da darajarsa ta kai naira miliyan 10.

A sharudan bayar da belin tuhuma ta biyu kuwa ga mutane biyar din da ake zargi da karkatar da naira miliyan 408 , za su gabatar da mutane biyu tare da yin takaddar rantsuwa da idan wanda ya tsayawa ya gudu zai biya naira miliyan 5, sannan za su ajiye naira miliyan 10, na biyu sai sun samo wanda yake da gida ko fili da darajarsa ta kai naira miliyan 200 a jahar Kano.

Advertisement

A karshe mai shari’a Mustapha Sa’ad Datti ya dage ci gaba da sauraran shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Fabarairu 2023.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending