News
ICPC Ta Kama Matar Da Ke Sayar Da Sabbin Kudi A Twitter
DAGA HAUWA KUNDILA
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa Kasa (ICPC) ta kama wata mata mai shafin Twitter mai suna @Simisola, kan zargin ta da sayar da sabbin takardar kudin Naira a shafukan sada zumunta.
Kakakin hukumar, Misis Azuka Ogugua a wata sanarwa , ta ce an kama matar ne sakamakon bayanan sirri da jami’an ICPC suka bankado.
Kotu Ta Bayar Da Belin Alkalan Kotunan Shari’ar Addinin Musilinci
Ta ce wadda ake zargin ta yi amfani da yanayin karancin sabbin takardun Naira wajen tallata hajarta a shafinta.
A cewarta, wadda ake zargin a halin yanzu tana tsare a hannun ICPC kuma tana taimaka wa hukumar wajen gano masu hannu a karancin sabbin kudaden da aka sauya wa fasali.
Ta bayyana kamun a matsayin wani shirin hadin gwiwa tsakanin CBN, ICPC da EFCC wajen aiwatar da sabon tsarin sauya fasalin takardun Naira.
