News
Sarkin Karaye: Mun Daɗe Muna Wayar Da Kan Jama’a, Amma Zuwan Kwamitin Ya Ƙara Mana Ƙaimi
Mai Martaba Sarkin Karaye, Alhaji Muhammad Maharazu, ya buƙaci Ƙaramin Kwamitin Kartakwana kan Rajistar Katin Zaɓe (CVR) da ya ci gaba da wayar da kan al’umma kan muhimmancin karɓar Katin Zaɓe na Dindindin (PVC) bayan kammala aikin rajista.
Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin Shugaban Ƙaramin Kwamitin Kartakwana kan Rajistar Katin Zaɓe (CVR) na Ɗan Malikin Kano, Kwamared Auwalu Mudi Yakasai, wanda ya jagoranci tawagar kwamitin zuwa Fadar Karaye domin neman goyon bayan masarautar wajen ƙarfafa wayar da kan jama’a kan muhimmancin rajistar katin zaɓe.
Ruwan Sama: Jihohi Sama Da 30 Na Fuskantar Barazanar Ambaliya — Gwamnatin Tarayya
Ya yabawa kwamitin bisa ƙoƙarin da yake yi na ƙarfafa al’umma su fito domin yin rajistar katin zaɓe, yana mai cewa wannan aiki ya ƙara wa masarautun gargajiya ƙarfin gwiwa wajen ci gaba da wayar da kan jama’a kan muhimmancin shiga harkokin dimokuraɗiyya.
Sarkin ya ce Masarautar Karaye ta daɗe tana ilmantar da al’umma kan muhimmancin mallakar katin zaɓe, amma ya jaddada cewa bai kamata aikin kwamitin ya tsaya kan rajista kaɗai ba.
A cewarsa, bayan an kammala rajistar katin zaɓe, ya dace kwamitin ya ƙaddamar da wani sabon gangamin wayar da kai kan muhimmancin karɓar Katin Zaɓe na Dindindin (PVC), domin tabbatar da cewa duk wanda ya yi rajista ya karɓi katinsa kuma ya yi amfani da shi wajen zaɓen shugabannin da yake so.
Ya ƙara da cewa rajista ba ta cika amfani ba idan ba a karɓi katin zaɓe ba, yana mai cewa karɓar katin da amfani da shi a ranar zaɓe su ne ginshiƙan tabbatar da dimokuraɗiyya da shugabanci nagari.
Tun da farko, Shugaban kwamitin, Kwamared Auwalu Mudi Yakasai, ya ce kwamitin na samun cikakken goyon bayan masarautun gargajiya a faɗin Jihar Kano, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen ƙara wayar da kan jama’a kan muhimmancin rajistar katin zaɓe.
