Connect with us

News

An Kama Wani Likitan Bogi Bisa Zargin Karɓar Haihuwa Da Safarar Jarirai

Published

on

Medical Health Doctor

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo ta kama wani mutum mai suna Osaze Okungbowa, mai shekara 46, bisa zargin yin aikin likita ba tare da cancanta ba tare da  karɓar haihuwa da kuma safarar jarirai.

An kama shi ne bayan wata mata mai suna Princess Oke ta kai ƙorafi cewa jaririn da ta haifa a ƙarƙashin kulawarsa ya ɓace.

Ruwan Sama: Jihohi Sama Da 30 Na Fuskantar Barazanar Ambaliya — Gwamnatin Tarayya

Da yake amsa tambayoyi a hedikwatar rundunar ’yan sandan jihar, wanda ake zargin ya amsa cewa ba ƙwararren likita ba ne, domin bai taɓa halartar jami’a ba. Ya ce ya samu horo ne kawai a matsayin mataimakin jinya, kuma yana aiki ne a wani asibiti mai zaman kansa.

Okungbowa ya ce ranar da aka kawo matar domin haihuwa bai samu damar karɓar haihuwar ba saboda rashin lafiya, don haka ya kira wata ungozoma ta taimaka.

Ya ƙara da cewa bayan haihuwar, an nemi a kai jaririn wani asibiti domin a saka shi a na’urar kula da jarirai, amma ya rasu a hanya, kafin daga bisani aka binne shi.

Advertisement

Sai dai mahaifiyar jaririn ta yi watsi da wannan bayani, tana mai cewa ta ji jaririn yana kuka bayan haihuwa kafin ta suma. Ta ce da ta farfaɗo ba ta ga jaririn ba, sai aka sanar da ita cewa ya mutu, lamarin da ta ce ba ta yarda da shi ba.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Edo, Monday Agbonika, ya tabbatar da cewa rundunar ta fara cikakken bincike kan lamarin, yana mai cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike domin tabbatar da adalci.

 

 

 

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending