Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 1,500 A  Cikin Watanni Shida

Published

on

‎Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya Da Take Rike Da Su Na Tsawon Kwanaki 10

Dakarun soji a sassan Najeriya sun kashe ƴan ta’adda dubu 1,597 tare da ceto mutane dubu 1,516 da aka yi garkuwa dasu cikin watanni shida na farkon shekarar 2026.

An sanar da wannan nasara ne yayin wani taron tsaro da aka gudanar a cibiyar yaƙi da ta’addanci a Abuja, inda mai magana da yawun rundunar sojin da wakilan sauran hukumomin tsaro 14 suka gabatar da rahotan ayyukansu.

An Kama Wani Mutum Bisa Zargin Sayar Da Ɗan Abokinsa Kan Naira Miliyan 1.3

A cewar mai magan da yawun rundunar Samaila Uba, sojojin sun kai hare-hare ta ƙasa da sama da kuma ta ruwa har sau dubu 14,221, tsakanin Janairu zuwa Yunin bana a faɗin yankunan ƙasar 6.

Hare-haren sun shafi kan ƴan ta’adda, da ƴan bindiga, da masu garkuwa da mutane, da masu satar mai ta hanyar fashe-fashen bututu, da dai sauran laifuffuka.

Yayin hare-haren, jami’an tsaron sun ƙwato bindigu 451, da alburusai dubu 16,726 dai dai sauran makamai da ƴan ta’addan ke amfani dasu..

Advertisement

 

 

RFI

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending