Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Kama Matashi Ɗan Shekara 15 Kan Zargin Hannu A Kisan Birgediya Janar A Borno

Published

on

15 year old Boko Haram suspect

Dakarun tsaro da ke aiki ƙarƙashin rundunar Operation Hadin Kai sun kama wani matashi ɗan kimanin shekara 15 da ake zargi da hannu a wani hari da ya yi sanadin mutuwar Birgediya Janar Oseni Braimah a Jihar Borno.

Majiyoyin tsaro sun shaida wa manema labarai cewa an cafke matashin, Tijjani Madu, ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa sayen abinci ga wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne a yankin.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Ta Ciyo Bashin Naira Tiriliyan 8 Da Biliyan 100 Cikin Watanni Uku Na Farkon 2026

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin matashin da hannu a harin da aka kai wani sansanin sojoji a ranar Alhamis, wanda ya yi sanadin mutuwar babban jami’in soja tare da wasu dakarun tsaro. Ana danganta harin da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram.

Advertisement

Wata majiya ta ce matashin ya amsa cewa ya taba shiga wasu hare-hare a yankunan Benisheik da Ngamdu, inda aka kashe jami’an tsaro da dama.

Haka kuma, an ce an kama shi ne bayan an turo shi daga Jilli da kuɗi kimanin Naira 850,000 domin sayo wasu kayan aiki.

Advertisement

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Masana tsaro na ci gaba da nuna damuwa kan yadda ake amfani da ƙananan yara a ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, lamarin da ke ƙara jefa al’umma cikin fargaba.

Advertisement

 

DAILY POST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending