News
Jami’an ’Yansanda Sun Kama Wani Mutum Bisa Zargin Hallaka Matar Aure A Kano
Rundunar ’yan sanda ta Jihar Kano ta kama wani mutum mai shekaru 41, Lucky Isuma, bisa zargin hannu a mutuwar wata matar aure a unguwar Sabon Gari.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin mutuwar matar, wadda aka bayyana sunanta da Sandra.
Jami’an ’Yan sanda Sun Kama Wani Mutum Bisa Zargin Hallaka Matar Aure A Kano
A cewarsa, lamarin ya faru ne a ranar 11 ga Afrilu, 2026, bayan da wani matashi mai suna Chidera Nwobi, mai shekaru 22, ya kai rahoto ofishin ’yan sanda na Sabon Gari cewa ya tarar da matar a kwance cikin ɗakin makwabcinsa ba ta motsi.
“Da misalin ƙarfe 10:30 na safe, mai kai rahoton ya bayyana cewa ya iske matar a kwance kan gado cikin halin rashin motsi a ɗakin makwabcinsa,” in ji sanarwar.
Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda sun isa wurin da abin ya faru, inda suka gudanar da bincike na farko a jikin mamaciyar, amma ba su gano wata alamar tashin hankali a jikinta ba.
Daga bisani, an kai ta Asibitin Koyarwa na Muhammadu Abdullahi Wase, inda likita ya tabbatar da rasuwarta.
Rundunar ta ce ana shirin gudanar da binciken gawar domin tantance ainihin dalilin mutuwar.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin a mika lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka (CID) domin gudanar da cikakken bincike.
