Connect with us

News

Tsaro Zai Inganta A Najeriya Bayan Babban Zaben 2027 — Godswil Akpabio

Published

on

majalisar
Akpbabio ya bayyana haka ne a yayin bikin kaddamar da ofshin Hukumar Tara Haraji ta Kasa (NRS) a Abuja, inda ya danganta matsalar tsaro da ta yi kamari a kasar a halin yanzu da kusantowar zaben 2027.

Ya kara da cewa Shugaba Tinubu yana gudanar da mulki cikin nagarta, inda ya zargi masu adawa da gwamnati da daukar nauyin tada rikice-rikice a kasar.

Advertisement

Jami’an ’Yansanda Sun Kama Wani Mutum Bisa Zargin Hallaka Matar Aure A Kano

Akpabio ya ce matsalar tsaro tana karuwa ne saboda zaben da ke tafe, amma nan da makonni biyu bayan kammala zabe za ta ragu.

Advertisement

Ya kuma yi ba’a ga ’yan adawa, musamman dan takarar jam’iyyar Labour a zaben shugaban kasa na 2023, Peter Obi, inda ya ce, “’yan adawa sun shiga rudani. Mutumin da ya samu kuri’u milyan shida ya sauya sheka daga jam’iyyar, yana zargin jam’iyya mai mulki.”

Akpabio ya roki ’yan Najeriya da su yi hakuri da gwamnatin Tinubu.

Advertisement

A wajen bikin kaddamar da sabon ginin hukumar haraji, Akpabio ya yi kirari ga shugaban hukumar, Dakta Zacch Adedeji, a yayin bikin, wanda ya samu halarcin mnayan jami’an gwamnati ciki har da Shugaba Bola Tinubu da ya kaddamar da ginin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Jibrin Barau, Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, da Mataimakin Kakakin Benjamin Kalu.

Sauran sun hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume, Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro Nuhu Ribadu, ministoci, da kuma gwamnoni daga jihohi daban-daban.

Advertisement

Gwamnonin da suka halarta sun hada da Babagana Zulum (Borno), Charles Soludo (Anambra), Caleb Mutfwang (Filato), Hope Uzodimma (Imo), da kuma Usman Ododo (Kogi).

Sabon ginin hukumar haraji da aka kaddamar, wanda aka bayyana a matsayin gini na zamani, yana da bene 16 tare da damar daukar ma’aikata kusan 3,000.

Advertisement

A watan Yuni 2025 ne Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan dokar kafa Hukumar Haraji ta Najeriya (NRS), wacce ta maye gurbin FIRS.

 

Advertisement

 

Aminiya

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending