Connect with us

News

Mutane 200 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Dakarun Sojin Sama Iyakar Yobe Da Borno

Published

on

Wani Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Hallaka Mutane Da Dama A Sokoto 

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya tabbatar da cewa harin sama da sojojin Najeriya suka kai ya shafi ƴan ta’adda da dama fiye da fararen hula.

A yayin da yake jawabi shugaban yace guraren da sojojin suka kai harin sanannun guraren taruwar ƴan ta’adda ne, kuma tun shekaru biyu da suka gabata ya bada umarnin kulle kasuwar, kasancewar ƴan ta’adda na Boko Haram ne suka mamayeta.

Advertisement

Kalaman na shugaban na zuwa ne a dai-dai lokacin da ƙungiyoyin fararen hula suka fara sukar rundunar sojin Najeriya kan harin da ta kai, inda ake zargin ya ƙare ne kan fararen hula.

Gwamnatin Tarayya Ta Ciyo Bashin Naira Tiriliyan 8 Da Biliyan 100 Cikin Watanni Uku Na Farkon 2026

Advertisement

Zuwa yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutane sama da 200 a wannan ruwan wuta, inda kuma aka ce mafi yawan waɗanda suka mutu ƴan kasuwa ne, yayinda da dama suka jikkata.

 

Advertisement

Lamarin ya faru ne a wasu yankuna da ke tsakanin kasuwar Jilli da Gubio sai kuma Gaidam a jihohin Yobe da Borno.

 

Advertisement

To sai dai kuma wani abu da ke ɗaure kai shine yadda rundunar sojin sama ta Najeriya ta bakin mai magana da yawunta Sani Uba ta ce harin ya faru ne bisa kuskure, amma duk da haka ya shafi ƴan ta’adda da dama.

 

Advertisement

Sanarwar ta ce duk da haka rundunar zata gudanar da bincike don gano dalilin wannan hari na kuskure kamar yadda ta ce da farko.

 

Advertisement

Gwamnan jihar ya sanar da cewa gwamnati ta jima tana gargaɗin fararen hula game da zuwa wannan kasuwa don gudun chakuɗuwar su da ƴan ta’adda gudun irin wannan mataki na soja, kasancewar ba’a samun labarin lokacin faruwarsa.

Wani ganau ya shaidawa manema labarai cewa aƙalla ƴan kasuwa 200 sun mutu a ƙauyen Jilli da ke mazaɓar Futchimiram ta ƙaramar hukumar Geidam, yana mai cewa harin ya faru ne da tsakar rana lokacin da ake tsakan da cin kasuwa.

Advertisement

 

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending