News
Gwamnatin Tarayya Ta Ciyo Bashin Naira Tiriliyan 8 Da Biliyan 100 Cikin Watanni Uku Na Farkon 2026
Gwamnatin Tarayya a Najeriya ta ciyo bashin Naira tiriliyan 8 da biliyan 100 (N8.1trn) a cikin watanni ukun farko na shekarar 2026, lamarin da ke nuna ƙaruwa a yawan bashin cikin gida fiye da yadda aka tsara a kasafin kuɗin shekarar.
Rahotanni sun nuna cewa wannan adadi ya zarce wanda aka samu a irin wannan lokaci na shekarar 2025, inda aka ciyo kusan Naira tiriliyan 7.5, abin da ke nuni da ƙarin kusan kashi 7.4 cikin ɗari a wannan shekara.
Jami’an ’Yansanda Sun Kama Matasa Biyu Kan Zargin Hallaka Abokinsu A Wurin Casu
Bincike ya nuna cewa ƙarin bashin na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙalubale ta fuskar ƙarancin kuɗaɗen shiga daga haraji, tare da ƙaruwa a buƙatun kuɗaɗen gudanar da ayyuka da samar da ababen more rayuwa.
Bayanai daga hukumomin kuɗi, ciki har da Babban Bankin Najeriya da Hukumar Kula da Bashin Ƙasa, sun bayyana cewa karɓar bashin na da nasaba da yadda ake tafiyar da harkokin kuɗaɗe a matakin gwamnati, musamman wajen rufe gibi a kasafin kuɗi.
Masana tattalin arziki na ci gaba da nuna damuwa kan yadda gwamnati ke ƙara dogaro da bashin wajen tafiyar da ayyukanta. A cewarsu, yawan karɓar bashin na iya ƙara jefa tattalin arzikin ƙasar cikin matsin lamba, musamman idan ba a samu ingantaccen tsarin ƙara yawan kuɗaɗen shiga ba.
Wani masani a fannin hada-hadar kuɗaɗe, Ifeanyi Ubah, ya bayyana cewa yawan dogaro da bashin na iya kawo cikas ga bunƙasar tattalin arziki, inda ya ce hakan na nuna gazawa wajen inganta hanyoyin samun kuɗaɗen shiga na cikin gida.
Masu sharhi sun jaddada buƙatar gwamnati ta mayar da hankali kan faɗaɗa hanyoyin tattara haraji da kuma rage kashe kuɗaɗe marasa muhimmanci, domin rage dogaro da bashin da kuma tabbatar da ɗorewar tattalin arziki.
