News
Kashi 7 Cikin 100 Na Kudin Sayen Makamai Kacal Aka Damka Wa Sojoji A 2025 —Rahoto
Alƙaluman da gwamnatin tarraya ta fitar sun nuna kashi 7 cikin 100 kacal na kasafin kuɗin da aka ware domin sayen makamai kawai aka damƙa wa Rundunar Sojin Ƙasa na Najeriya.
Daga cikin Naira biliyan 34.71 da aka ware wa gyaran jiragen yaƙi na Rundunar Sojin Sama, Naira biliyan 4.85 kacal (kashi 13.98%) aka fitar. Ba a saki ko sisi ba domin man motocin sufuri da na jiragen sama da ɗaukar ma’aikata da gina barikin soja da bincike da bunƙasa aiki.
Gobara Ta Lakume Albasar Sama Da Naira Miliyan 56 A Sakkwato
Daga cikin Naira biliyan 15.75 da aka ware wa sayen kayan tsaro na Rundunar, an saki Naira biliyan 5.25 (kashi 33.33%). Amma sayen kayan kare ƙasa ya samu koma baya sosai, inda aka saki Naira biliyan 19.25 kacal (kashi 6.45%) daga cikin Naira biliyan 298.44 da aka ware.
Kasafin Naira biliyan 117.90 na gyaran kayan tsaro ya samu kashi 3.99% (Naira biliyan 4.71), amma ba a saki ko sisi ba domin ginawa da samar da kayan tsaro (Naira biliyan 7.16). Kula da jin daɗin sojoji (Naira miliyan 28.33) bai samu ko sisi ba, haka ma gina barikin soja (Naira miliyan 95.68), gyaran barikin soja (Naira biliyan 6.76) da kuɗin mai na wasu motocin sufuri (Naira miliyan 45.03), duk ba su samu ko sisi ba.
Sauran muhimman abubuwa da suka samu ƙarancin kulawa sun haɗa da kuɗin mai na jiragen sama (Naira biliyan 2.23 daga cikin Naira biliyan 43.91 – kashi 5.07%), kudin mai na motocin aiki (Naira biliyan 1.71 daga cikin Naira biliyan 4.41 – kashi 38.72%) da horon kasashen waje (Naira biliyan 2.20 daga cikin Naira biliyan 17.56 – kashi 12.50%).
Sai dai horon cikin gida, gyaran motocin aiki, hidimar tsaro da kuɗin tsaro sun samu aiwatarwa mai gwaɓi da kashi 41.56%, 58.28%, 98.10% da 79.65% bi da bi.
Ƙoƙarin da aka yi jiya wajen jin ta bakin rundunar tsaro kan aiwatar da kasafin bai yi nasara ba, domin kira da aka yi wa Daraktan Hulɗar Soja, Birgediya Janar Samaila Uba, bai ɗauka ba, kuma bai amsa rubutattun sakonnin tes da na WhatsApp da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.
