Connect with us

News

Jami’an Hukumar NDLEA Sun Kama Bama-bamai 942 A  Zamfara

Published

on

WhatsApp Image 2025 05 04 at 12.03.28 750x430 (1)

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama bama-bamai 942 da aka boye a cikin wata mota da ke kan hanyarta daga Nasarawa zuwa Zamfara.

An motar ce a ranar Asabar, 3 ga watan Mayu, yayin sintirin da jami’an hukumar suka yi a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Advertisement

Duk Wanda Ke Tunanin Wulakanta Kwankwaso Shi Ne Zai Wulakanta — Gwamnan Kano

Hukumar ta ce an gano bama-baman ne bayan da aka binciki motar kirar haya. Haka kuma an kama wani mutum mai shekaru 30 da ake zargi da hannu a safarar bama-baman, wanda aka bayyana da suna Nura Sani Muhammad, wanda aka fi sani da Nura Hariji.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.

Advertisement

Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (Rtd), ya bada umarnin a mika wanda ake zargi ga hukumomin tsaro da suka dace domin ci gaba da bincike.

A wani samame da jami’an hukumar suka yi a Kano a ranar Laraba, 30 ga Afrilu, an kama wasu mutane biyar da ake zargi da safarar kwayoyi a kasuwar Dangoro, bisa jagorancin wani matashi mai suna Aminu Musa (aka Kadagi). An same su da bulo 50 na tabar skunk mai nauyin kilogiram 21.6.

Advertisement

Haka kuma, a jihar Edo, jami’an NDLEA sun kama wata motar haya kirar Toyota bas da ke dauke da kwayoyi iri-iri daga Onitsha, jihar Anambra zuwa Auchi.

Kwayoyin da aka kwato daga motar sun hada da: tramadol 314,020, rophynol, diazepam, exol5, kwalabe 638 na syrup mai codeine, da kuma ampoules 200 na allurar pentazocine.

Advertisement

Hukumar ta ce za ta ci gaba da kai farmaki kan masu safarar miyagun kwayoyi da duk wani abu da ke barazana ga tsaron kasa.

 

Advertisement

 

SOLACEBASE 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending