News
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wata Mata mai Shekaru 30 Da Katunan ATM 88
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta kama wata mata mai shekara 30, Success Olafemi, bisa zargin ƙoƙarin jan hankalin wata yarinya ’yar shekara bakwai, yayin da jami’an tsaro suka gano katunan ATM 88 mallakin bankuna da cibiyoyin hada-hadar kuɗi daban-daban a hannunta.
An kama matar ne a ranar Asabar, 22 ga Agusta, 2026, a yankin Kara Makasia, kusa da sansanin Redeemed Christian Church of God (RCCG) da ke Jihar Ogun.
Dalilin Da Suka Jawo Yara Sama Da 870,000 Ba Sa Zuwa Makaranta A Kano — Rahoto
Rahotanni sun ce wata mata mai suna Tope Makinde, mazauniyar ƙauyen Iwe-Lepe da ke kan hanyar Sagamu, ce ta sanar da ’yan sanda lamarin da misalin ƙarfe 10:00 na safe.
Makinde ta shaida wa ’yan sandan cewa Olafemi ta je Ewu-Lisa ta Simawa da misalin ƙarfe 9:00 na safe, inda ake zargin ta yi ƙoƙarin jan hankalin wata yarinya mai suna Jumat, wadda ba a bayyana cikakken sunanta ba.
A cewar rahoton, wadda ake zargin ta yi amfani da takardun kuɗin Naira 200 da kuma ƙananan Milo wajen jan hankalin yarinyar, kafin daga bisani aka cafke ta.
Bayan gudanar da bincike, jami’an ’yan sanda sun gano katunan ATM 88 a cikin kayanta. Katunan sun haɗa da 25 na OPay, 13 na UBA, biyu na Skye Bank, bakwai na Keystone Bank, tara na GTBank, 10 na Zenith Bank, biyu na PalmPay, huɗu na Ecobank da 11 na First Bank.
Baya ga katunan ATM ɗin, an kuma gano N7,000 a tsabar kuɗi, mafi yawansu takardun N200, tare da Milo da Nescafé a cikin jakarta.
Rahoton ya ce yayin da jami’an tsaro ke yi mata tambayoyi, Olafemi ta kasa bayar da gamsasshen bayani kan yadda ta mallaki katunan ATM ɗin masu yawa.
A halin yanzu, ana tsare da wadda ake zargin a hannun ’yan sanda, yayin da jami’an bincike ke ci gaba da gudanar da bincike domin gano asalin katunan da kuma tabbatar da gaskiyar zargin da ake mata dangane da yarinyar.
’Yan sanda na kuma ƙoƙarin gano ko katunan ATM ɗin suna da alaƙa da wasu laifuka.
