Connect with us

News

Farashin Mai Ya Tashi Bayan Trump Ya Janye Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Da Iran

Published

on

FB IMG 1773006543246

Farashin ɗanyen man fetur ya yi tashin gwauron zabo da kashi biyar cikin ɗari (5%) a ranar Laraba, bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da janye yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma tsakanin Amurka da Iran kan tsagaita wuta.

Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake halartar taron ƙungiyar tsaro ta NATO a birnin Ankara na ƙasar Turkiyya. Ya kuma yi barazanar kai sabbin hare-hare kan Iran, lamarin da ya ƙara haifar da fargaba kan makomar zaman lafiyar yankin da kuma ƙoƙarin da masu shiga tsakani ke yi na sasanta rikicin.

Kotu Ta Yanke Wa Direban Adaidaita Sahu Hukuncin Daurin Rai Da Rai 

Matakin na Trump ya biyo bayan hare-haren da dakarun Juyin Juya Halin Iran suka kai kan sansanonin sojojin Amurka da ke ƙasashen Kuwait da Bahrain, a matsayin martani ga farmakin da Amurka ta kai wa Iran. A baya dai gwamnatin Amurka ta zargi Iran da kai hare-hare kan wasu jiragen dakon mai a mashigin ruwan Hormuz.

Bayan wannan sabon tashin hankali, farashin gangar ɗanyen mai ya haura zuwa dala 78, wanda shi ne mafi girman ƙarin da aka samu cikin rana guda tun ƙarshen watan Mayun bana.

Haka kuma, kasuwannin hada-hadar hannayen jari sun fuskanci koma baya, inda manyan kamfanoni a Turai suka yi asarar kusan kashi 1.6 cikin ɗari, yayin da wasu kamfanoni a Amurka suka yi asarar tsakanin kashi 1 zuwa 1.3 cikin ɗari.

Advertisement

Masana tattalin arziƙi sun bayyana cewa, duk da cewa farashin mai bai kai matakin sama da dala 120 kan kowace ganga kamar yadda aka gani a lokacin da rikicin Amurka da Iran ya yi ƙamari ba, sabon tashin farashin na iya yin illa ga tattalin arziƙin duniya da ke ƙoƙarin farfaɗowa bayan matsalolin ƙarancin makamashi da aka fuskanta a sassa daban-daban na duniya.

 

RFI

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending