News
Cutar Zazzabin Lassa Ya Hallaka Mutane 263 A Jihohi 24 —NCDC
Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ce mutane 263 ne suka mutu sakamakon zazzabin Lassa a ƙasar tsakanin watan Janairu da Satumba na shekarar 2026.
Hukumar ta bayyana cewa an tabbatar da mutane 1,115 sun kamu da cutar a jihohi 24, yayin da cutar ta yaɗu zuwa ƙananan hukumomi 119.
2027: Ƙungiyar Da Hannu Na Ta Nemi Gwamnan Bauchi Bala Mohammed Ya Goyi Bayan Shugaba Tinubu
Rahoton NCDC na makon cututtuka na 38, wanda ya shafi tsakanin 14 zuwa 20 ga Satumba, ya nuna cewa yawan mutuwar waɗanda suka kamu da cutar ya kai kashi 23.6 cikin 100.
Wannan adadi ya haura na makamancin lokacin shekarar 2025, lokacin da yawan mutuwar ya kai kashi 18.5 cikin 100.
Sai dai hukumar ta ce an samu raguwar sabbin masu kamuwa da cutar, inda aka tabbatar da mutum 11 a makon da ake nazari, sabanin mutum 17 da aka samu a makon da ya gabata.
Jihohin Ondo, Edo da Taraba ne suka samu sabbin masu kamuwa da cutar a wannan mako.
NCDC ta ce kashi 87 cikin 100 na waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar sun fito ne daga jihohin Bauchi, Ondo, Taraba, Benue da Edo.
Hukumar ta kuma bayyana cewa mutanen da shekarunsu ke tsakanin 21 zuwa 30 ne suka fi kamuwa da cutar.
A cewar rahoton, ba a samu sabon ma’aikacin lafiya da ya kamu da cutar ba.
Zazzabin Lassa cuta ce da ake iya ɗauka ta hanyar taɓa abinci ko kayan amfanin gida da bera mai ɗauke da cutar ya gurɓata. Haka kuma, cutar na iya yaɗuwa daga mutum zuwa mutum, musamman a wuraren jinya idan ba a kiyaye matakan kariya yadda ya kamata ba.
