Connect with us

News

Kansilar Da Aka Sace Ta Rasu A Hannun Waɗanda Suka Sace Ta A Kogi

Published

on

IMG 20261009 212748

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe Kansila Rosemary Adukwu, wadda ke wakiltar Mazaɓar Ogugu Ward III a Ƙaramar Hukumar Olamaboro ta Jihar Kogi, kwanaki bayan sun yi garkuwa da ita.

An sace Adukwu ne a ranar 30 ga Satumba, 2026, lokacin da take kan hanyarta ta zuwa kasuwar Onitsha da ke Jihar Anambra.

Cutar Zazzabin Lassa Ya Hallaka Mutane 263 A Jihohi 24 —NCDC

Rahotanni sun ce waɗanda ake zargin masu garkuwa ne sun tare motar da take ciki a kusa da Oji River, tsakanin jihohin Enugu da Anambra, inda suka tafi da ita, yayin da suka bar sauran fasinjojin.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Olamaboro, Dakta Ameh Williams, ne ya tabbatar da rasuwarta a ranar Juma’a, inda ya ce an tabbatar da mutuwarta ne a ranar Alhamis, lokacin da take hannun masu garkuwar.

Iyalanta sun bayyana cewa waɗanda suka sace ta ba su tuntuɓe su domin neman kuɗin fansa ba tun bayan sace ta.

Advertisement

Sun kuma ce an kama direban motar da take ciki, tare da wani mutum da ya amsa kiran da aka yi wa wayarta, domin taimaka wa ‘yan sanda wajen gudanar da bincike kan lamarin.

A nasa ɓangaren, Shugaban Ƙungiyar Ci Gaban Gundumar Ogugu, Deacon Samuel Ige Agada, ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai bayyana shi a matsayin mummunan aiki.

Agada ya bayyana marigayiyar a matsayin ‘yar kasuwa mai jajircewa da kuma jagorar al’umma, yana mai cewa mutuwarta ta jefa iyalanta cikin babban baƙin ciki.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kogi ba ta fitar da sanarwa a hukumance dangane da kisan ba.

An yi jana’izar marigayiyar a gidanta da ke Cibiyar Ogugu a ranar Juma’a.

 

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending