News
Gwamnatin Benue Ta Rufe Makarantu Kan Tilasta Wa Iyaye Sayen Littattafai
Gwamnatin Jihar Benue ta rufe wasu makarantu biyu bisa zargin tilasta wa iyaye sayen littattafan karatu daga makarantun, tare da hukunta ɗaliban da suka sayi littattafai daga wasu shaguna.
Hukumar Kula da Ingancin Ilimi da Jarabawa ta Jihar Benue (BEQAEB) ce ta rufe makarantun Orenda da Opal, bisa zargin cin zarafin ɗalibai da karya dokokin gwamnati kan saye da sake amfani da littattafan karatu.
Gwamnatin Benue Ta Rufe Makarantu Kan Tilasta Wa Iyaye Sayen Littattafai
Sakataren zartarwar hukumar, Dr Terna Francis, ya ce matakin ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da iyaye suka shigar, inda suka zargi makarantun da tilasta musu sayen littattafai daga wurinsu, tare da hukunta ɗaliban da iyayensu suka sayi littattafan daga wasu shaguna.
Dr Francis ya kuma zargi mai makarantun, Onyinye Okoye, da wasu ma’aikatan makarantar da cin zarafin jami’an hukumar tare da lalata motarsu a lokacin da suke aiwatar da umarnin kotu.
Ya ce an ɗauki matakin ne domin tabbatar da bin dokokin gwamnati da kare haƙƙin ɗalibai da iyayensu.
Hukumar ta bayyana cewa makarantun biyu za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai sun cika sharuɗɗan da aka gindaya tare da tabbatar da bin ƙa’idojin gwamnati.
