News
Guguwar Iska Mai Karfi Ta Hallaka Mutum 7, Yayin Da Fiye Da Mutum 5,400 Ke Cikin Mawuyacin Hali A Jigawa
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA) ta ce mutum bakwai sun rasu, yayin da mutum 5,403 suka shiga cikin mawuyacin Hali sakamakon guguwar iska mai ƙarfi da ruwan sama da suka afku a sassa daban-daban na jihar.
Sakataren Zartarwa na hukumar, Hannafi Yakubu ne , ya shaida wa manema labarai a Dutse cewa lamarin ya shafi al’ummomi 120 da ke cikin ƙananan hukumomi 13 na jihar.
Farashin Mai Ya Tashi Bayan Trump Ya Janye Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Da Iran
A cewarsa, guguwar ta lalata makarantu 47 na gwamnati, cibiyoyin lafiya uku da kuma ofisoshin ‘yan sanda biyu. Ya ƙara da cewa an tattara waɗannan bayanai ne tun daga farkon daminar bana zuwa yanzu.
Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Dutse, Gwaram, Birnin Kudu, Kiyawa, Babura, Gumel, Kaugama, Ringim, Gagarawa, Kirikasamma, Sule Tankarkar, Miga da Buji.
Hannafi Yakubu ya ce gwamnatin jihar ta fara raba kayan agaji ga mutanen da lamarin ya shafa domin rage musu raɗaɗin halin dasuke ciki.
NAN
-
News2 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News3 days ago
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
-
News2 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
