News
Ku Fara Harbe Yan Bindiga Kafin Karbar Umarni — Ministan Tsaro Christopher Musa Ga Dakarun Soji
Ku Fara Harbe Yan Bindiga Kafin Karbar Umarni — Ministan Tsaro Christopher Musa Ga Dakarun Soji
Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya umarci jami’an tsaro da ke fafatawa da ’yan ta’adda da ’yan bindiga da kada su yi jinkirin ɗaukar mataki idan suka ci karo da masu ɗauke da makamai.
Ya ce duk jami’in da aka tura aiki amma ya ƙi fuskantar ’yan ta’adda ko ’yan bindiga da sunan yana jiran umarni, za a ɗauke shi tamkar yana taimaka wa maƙiya.
Mazauna Dorayi Karama Sun Roƙi Gwamnatin Kano Ta Kawo Musu Ɗauki Kan Matsalar Ambaliyar Ruwa
Christopher Musa ya bayyana hakan ne a birnin Sokoto yayin ƙaddamar da motocin sulke da sauran kayan aikin tsaro da gwamnatin jihar ta saya domin ƙarfafa yaƙi da matsalar rashin tsaro.
Ya jaddada cewa duk jami’in da aka tura bakin aiki yana da ikon kare kansa da kuma rayukan al’umma, don haka bai kamata ya jira wani sabon umarni kafin ya fuskanci ’yan bindiga ko ’yan ta’adda ba idan sun bayyana.
Ministan ya kuma buƙaci jami’an tsaron su yi amfani da sabbin kayan aikin yadda ya kamata, yana mai cewa gwamnati ta kashe kuɗaɗe masu yawa wajen samar da su domin ƙarfafa yaƙi da rashin tsaro a sassan ƙasar.
-
Uncategorized6 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News5 days agoAƙalla Mutane 40 Sun Mutu Bayan Kifewar kwale-kwale A Sokoto
-
News22 hours ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
