News
Kotu Ta Bayar Da Umarnin Tsare Malamin Jamiar Da Ya Zargi Gwamnatin Katsina Da Daukar Nauyin Yan Bindiga Zuwa Aikin Hajji
Kotun Majistare da ke Jihar Katsina ta bayar da umarnin tsare malamin Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Dr. Bashir Kurfi, bayan rundunar ‘yan sandan jihar ta gurfanar da shi bisa zargin bata suna da yaɗa bayanan da suka saba da gaskiya.
Alƙalin kotun, Zaharaddeen Kofar Soro, ya bayar da umarnin ne bayan ‘yan sanda sun shigar da ƙara kan Dr. Kurfi, inda suka zarge shi da aikata laifukan da suka shafi bata suna da yaɗa bayanan da za su iya cutar da martabar Gwamnatin Jihar Katsina da al’ummarta.
A cewar takardar ƙarar farko (FIR), Dr. Kurfi, wanda malami ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya yi kalaman ne yayin wata hira da Trust TV a ranar 24 ga Yunin 2026, inda aka ce ya yi zargin cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauki nauyin aikin Hajji ga wasu shugabannin ‘yan bindiga.
Masu gabatar da ƙara sun bayyana cewa zargin da malamin ya yi ƙarya ne, mai cike da mugun nufi, kuma zai iya bata sunan gwamnati tare da rage martabar jihar a idon jama’a.
Lokacin da aka karanta masa tuhume-tuhumen da ake masa ƙarƙashin sashe na 308 da 309(1) na Dokar Penal Code ta Jihar Katsina, Dr. Kurfi ya musanta dukkan zarge-zargen.
Bayan haka, lauyan gwamnati ya buƙaci kotu ta ba da umarnin ci gaba da tsare wanda ake tuhuma domin bai wa ‘yan sanda damar kammala bincike, yana mai cewa sakin sa da beli na iya kawo cikas ga binciken.
Sai dai lauyan wanda ake ƙara, A.D. Umar, ya yi adawa da wannan buƙata, inda ya roƙi kotun ta ba wanda yake karewa beli, yana mai jaddada cewa yana da haƙƙin samun ‘yanci har sai an same shi da laifi.
Bayan sauraron ɓangarorin biyu, Alƙali Zaharaddeen Kofar Soro ya umarci rundunar ‘yan sanda da ta ci gaba da bincike, sannan ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare Dr. Bashir Kurfi a hannun ‘yan sanda har zuwa ranar Litinin, 14 ga Yulin 2026, domin ci gaba da sauraron shari’ar.
A wani ci gaba mai alaƙa da lamarin, kwanaki kaɗan bayan kalaman Dr. Kurfi, Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama wasu da ake zargin shugabannin ‘yan bindiga ne da suka dawo daga aikin Hajji ta Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina.
-
News1 day ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News2 days ago
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
-
News2 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
