News
Rikici Ya Barke A Majalisar Wakilai Kan Buƙatar Gayyatar Shugaba Tinubu
An samu zaman cike da cece-kuce a Majalisar Wakilan Tarayya a yau ranar Laraba bayan wasu ‘yan majalisar sun yi sabani kan wani ƙuduri da ke neman a gayyaci Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, domin ya yi bayani kan wasu batutuwa da suka shafi kuɗaɗen gwamnati.
Hatsaniyar ta fara ne a yayin zaman majalisar lokacin da ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Okpe/Sapele/Uvwie ta jihar Delta, Benedict Etanabene, ya tashi da batun gaggawa (Point of Privilege).
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Wani Sufeton Bogi
Etanabene ya jawo hankalin majalisar zuwa wata takarda da Akanta Janar na Tarayya, Shamseldeen Ogunjimi, ya fitar a ranar 29 ga Yuni, wadda ta shafi wasu muhimman batutuwan gudanar da kuɗaɗen gwamnati.
Sai dai yayin da aka fara tattaunawa kan buƙatar gayyatar Shugaba Tinubu, wasu ‘yan majalisar sun nuna adawa da hakan, yayin da wasu kuma suka goyi bayan a ci gaba da tattaunawa.
Wannan ya janyo hayaniya da cacar baki a zauren majalisar, lamarin da ya sa aka ɗan dakatar da zaman na wani lokaci kafin a ci gaba.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a cimma matsaya ta ƙarshe kan ko za a gayyaci Shugaba Tinubu ko a’a ba.
-
News1 day ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News2 days ago
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
-
News2 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
