News
Kotu Ta Yanke Wa Direban Adaidaita Sahu Hukuncin Daurin Rai Da Rai
Babbar Kotun Jihar Akwa Ibom ta yanke wa wani direban Adaidaita Sahu mai suna Michael Effiong Japhet hukuncin daurin rai da rai bayan ta same shi da laifin fyade da kuma sata.
Mai shari’a Archibong Archibong ya bayyana cewa kotun ta gamsu da hujjojin da masu gabatar da kara suka gabatar, inda ta tabbatar da cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifukan da ake zarginsa da su.
Ku Fara Harbe Yan Bindiga Kafin Karbar Umarni — Ministan Tsaro
Kotun ta ce an yanke masa hukuncin ne bisa tanade-tanaden dokar laifukan fyade ta Jihar Akwa Ibom ta shekarar 2000, bayan an same shi da laifin yi wa wata mata fyade tare da kwace mata kudaden da ke hannunta.
Bayanan shari’ar sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 23 ga watan Fabrairun 2015, lokacin da wanda aka yankewa hukuncin ya dauki wata mata mai sayar da kayan marmari daga Ekom Iman zuwa Iko Ofon da ke cikin Karamar Hukumar Ikono. Sai dai maimakon ya kai ta inda ta nufa, ya karkatar da ita zuwa wani wuri da ba kowa kafin ya aikata laifin fyade a kanta.
Bugu da kari, kotun ta ji cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya kuma kwace jakarta mai dauke da Naira 7,000, kudin cinikin ranar matar, duk da rokon da ta yi masa kada ya cutar da ita. Bayan nazarin dukkan shaidu da hujjoji, kotun ta same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin daurin rai da rai.
-
Uncategorized6 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News5 days ago
Aƙalla Mutane 40 Sun Mutu Bayan Kifewar kwale-kwale A Sokoto
-
News1 day ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
