Labarai
KANO: ’Yan Takarar Gwamna 16 Na Jam’iyyun Adawa Sun Haɗa Kai Domin Kalubalantar APC A Zaɓen 2027

Gamayyar ’yan takarar gwamnan jihar Kano daga jam’iyyun adawa (CKSOGCF) ta bayyana cewa ta kulla yarjejeniyar haɗa kai domin tsayar da ɗan takara guda da zai fafata da jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2027.
Ɗan takarar gwamnan Kano a ƙarƙashin jam’iyyar PRP, Nasiru Hassan Koguna, ne ya bayyana hakan a madadin ƙungiyar yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano ranar Asabar.
Hukumar Shari’a Ta Kano Ta Nemi Haɗin Gwiwar ’Yan Jarida Wajen Yaƙi Da Cin Mutunci A Soshiyal Midiya
Koguna ya ce ’yan takarar gwamnan da ke cikin ƙawancen sun rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta wajabta musu yin aiki tare domin kawo sauyi a jihar.
Ya ce yarjejeniyar ba ta tsaya ga sanya hannu a takarda kawai ba, domin sun ɗauki alƙawarin haɗin kai a gaban Allah da al’ummar Kano.
A cewar ƙungiyar, duk da dumbin arzikin da jihar ke da shi, Kano na fama da matsalolin rashin aikin yi, ƙarancin tallafi ga mata ’yan kasuwa, koma bayan harkokin noma da kuma ƙarancin kulawa ga asibitoci da ɗalibai.
Ta bayyana cewa jihar na da arzikin ɗan Adam, kasuwanci, al’adu, addini da tarihi, amma tana buƙatar shugabancin da zai fifita muradun al’umma.
Ƙungiyar ta ce tsawon lokaci siyasar Kano ta kasance cikin rarrabuwar kawuna, inda muradun wasu tsirarun mutane suka rinjayi muradun al’umma.
Haka kuma, ƙawancen ya zargi jam’iyya mai mulki da hana jam’iyyun adawa damar sanya allunan tallan siyasa da sauran kayan yaƙin neman zaɓe a wuraren da aka tanada.
Ya ce yana da hujjojin da ke nuna cewa ana hana jam’iyyun adawa sanya allunan tallansu, yayin da ake barin jam’iyya mai mulki ta sanya nata.
Ƙungiyar ta bayyana cewa wannan mataki ya saɓa wa kundin tsarin mulki da ƙa’idojin dimokuraɗiyya, tana mai zargin cewa hakan na iya zama yunƙurin mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya guda.
Sai dai ta ce ba ta da niyyar tunzura jama’a, kuma za ta ci gaba da amfani da hanyoyin lumana wajen neman haƙƙinta da inganta zaman lafiya a jihar.
Ƙawancen ya kuma yi kira ga sauran jam’iyyun adawa da su shiga cikinsa domin haɗa ƙarfi wajen samar da ci gaba a Kano.
Ya ƙara da cewa har yanzu bai yanke shawarar ɗan takara ko jam’iyyar da zai mara wa baya a zaɓen gwamnan jihar na 2027 ba.
Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa jam’iyyun siyasa 16 ne suka kafa ƙawancen, ciki har da PRP, PDP, LP, ZLP, AAC, AA, YPP, ADP da APGA, da sauran jam’iyyu.
-
Labarai6 days ago
Dakarun Soji Sun Kuɓutar Da Yara 18 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna
-
Labarai3 days ago
BAYAN WATA SHIDA: Shugaba Tinubu Ya Yi Alƙawarin Kuɓutar da Ɗaliban Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Borno
-
Wassanni5 days ago
Najeriya Ba Ta Kai Matsayin Da Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Kofin Duniya Ba —Shugaban FIFA
