Connect with us

Labarai

Hukumar Shari’a Ta Kano Ta Nemi Haɗin Gwiwar ’Yan Jarida Wajen Yaƙi Da Cin Mutunci A Soshiyal Midiya

Published

on

1660769066062 (1)
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta nemi haɗin gwiwar Ƙungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo ta Kano Online Chapel (KOMC) daks ƙarƙashin ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), domin taimakawa wajen yaƙi da yaɗuwar kalaman cin mutunci, ɓatanci da saƙonnin da ka iya haddasa rikici a shafukan sada zumunta.

Kwamishinan Hukumar Shari’a ta Jihar Kano, Sheikh Ali Dan Abba, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa ta musamman da shugabanni da mambobin ƙungiyar Kano Online Media Chapel a ranar Alhamis, 26 ga Nuwamba, 2026.

Gwamnatin Tarrayya Za Ta Bai Wa Teloli 600 Tallafin Naira Miliyan 5 Kowannensu

Sheikh Ali Dan Abba ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu mutane ke amfani da shafukan sada zumunta wajen cin mutuncin juna, yaɗa labaran ƙarya da wallafa kalaman tunzura jama’a waɗanda ka iya kawo cikas ga zaman lafiya da haɗin kan al’umma.

Ya jaddada cewa damuwar hukumar ba ta shafi ƙwararrun ’yan jarida da kafafen yaɗa labarai masu bin ƙa’idojin aikin jarida ba, sai dai mutanen da ke amfani da shafukan sada zumunta wajen yaɗa abubuwan da ka iya haddasa fitina da rarrabuwar kawuna.

Kwamishinan ya buƙaci masu amfani da shafukan sada zumunta da su riƙa taka-tsantsan wajen wallafa bayanai, tare da tabbatar da sahihancin duk abin da suke yaɗawa domin kauce wa illolin da hakan ka iya haifarwa.

Advertisement

A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar Kano Online Media Chapel, Comrade Abubakar Dangambo, ya amince da damuwar da hukumar ta bayyana, inda ya ce matsalar yaɗa bayanan ƙarya da cin mutunci ta zama babban ƙalubale ga aikin jarida a intanet.

Dangambo ya bayyana cewa wasu mutane na zaune a gidajensu suna ƙirƙirar labarai ba tare da tantance sahihancinsu ba, sannan su yaɗa su a shafukan sada zumunta, lamarin da ke kawo cikas ga kafafen yaɗa labarai masu bin ƙa’idojin aikin jarida.

Ya ce irin wannan dabi’a na iya lalata martabar aikin jarida da kuma rage amincewar jama’a da kafafen yaɗa labarai, musamman wajen bambance sahihan rahotanni da bayanan ƙarya.

Shugaban ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumar da ƙungiyar ’yan jarida wajen wayar da kan jama’a kan amfani da shafukan sada zumunta cikin mutunci da sanin ya kamata.

Ya kuma nuna cewa ya kamata a bambance aikin jarida na ƙwararru da wallafe-wallafen mutanen da ba sa bin ƙa’idojin aikin jarida.

Haɗin gwiwar na zuwa ne a daidai lokacin da shafukan sada zumunta suka zama muhimmin dandali na yaɗa labarai, muhawara da sadarwa a tsakanin al’umma.

Advertisement

Sai dai duk wani matakin da za a ɗauka wajen magance matsalar ya kamata ya kasance bisa doka, tare da mutunta ‘yancin faɗin albarkacin baki da kuma damar ’yan jarida na gudanar da bincike da bayyana ra’ayoyi kan al’amuran da suka shafi jama’a.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending