Labarai
An Hallaka Wani Mutum Har Lahira Kan Gyaran Takalmi A Kano

Babbar Kotun Jihar Kano da ke kan titin Miller ta fara sauraron shaidu a shari’ar Nazifi Muhammad, wanda ake zargi da kashe Ismail Musa sakamakon saɓani da ya shiga tsakaninsu kan gyaran takalmi.
A zaman kotun da Mai Shari’a Abdu Maiwada ya jagoranta, lauyan masu gabatar da ƙara, Barrista Gazzali Mai-Gari Bichi, ya gabatar da shaidar farko mai suna Muhammad Usman.
Shaidan, wanda shi ma mai gyaran takalmi ne, ya bayyana cewa yana wurin da ake zargin lamarin ya faru, inda ya gabatar da bayanansa a gaban kotun.
Ana zargin Nazifi Muhammad Sauna da soka wa Ismail Musa almakashi a lokacin da suka samu saɓani kan aikin gyaran takalmi a unguwar Sauna da ke Kano.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a shekarar 2022.
Bayan sauraron shaidar, Mai Shari’a Abdu Maiwada ya ɗage shari’ar zuwa ranar 9 ga watan Fabrairu, 2027, domin ci gaba da sauraron shaidu.
