Connect with us

News

NDLEA Ta Sake Kama Wata Tsohuwa Mai Shekara 83 Kan Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi

Published

on

IMG 20261011 225903 500

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta sake kama wata tsohuwa mai shekaru 83, mai suna Uloma Uchechi Sunday, bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Jihar Abia.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 11 ga Oktoba, 2026.

Jami’ar Azare Za Ta Bai Wa Tsohon Ministan Ilimi, Adamu Adamu, Digirin Girmamawa

A cewar sanarwar, jami’an hukumar sun kama tsohuwar ne ranar Laraba, 7 ga Oktoba, a gidanta da ke Ite-Uzo, Umuaguma, Ƙaramar Hukumar Obingwa ta Jihar Abia.

An ce jami’an sun same ta da wasu miyagun ƙwayoyi da suka haɗa da methamphetamine da tabar wiwi ta Colorado, waɗanda ake zargin ta ɗaure a kugunta da zani.

Babafemi ya ce an sake kama tsohuwar ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa tana gudanar da wani wurin sayar da miyagun ƙwayoyi, wanda ake zargin wasu masu aikata laifuka a yankin ke ziyarta.

Advertisement

Ya bayyana cewa jami’an NDLEA sun taɓa kama Uloma tare da ’yarta mai shekaru 32, Chisom Uchechi, a wannan gida ranar 17 ga Mayun 2025.

A lokacin kamen na farko, hukumar ta ce ta ƙwato gram 50 na methamphetamine, gram 522 na tabar wiwi da aka sarrafa da aka fi sani da skunk, gram 260 na ganyen tabar wiwi da kuma gram 12 na tramadol.

Sanarwar ta ƙara da cewa mahaifiyar da ’yarta sun amsa laifukansu a gaban kotu, inda aka yanke wa kowannensu hukuncin ɗaurin watanni 12 a gidan yari ko kuma biyan tarar Naira 200,000.

Sai dai, a cewar hukumar, sun biya tarar da aka ci su, wanda ya ba su damar komawa gida.

NDLEA ta yi zargin cewa bayan an sake ta, Uloma ta koma harkar safarar miyagun ƙwayoyi, har ma ta kafa wani wurin sayar da su.

 

Advertisement

 

CHANNELSTV

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending