News
Jami’ar Azare Za Ta Bai Wa Tsohon Ministan Ilimi, Adamu Adamu, Digirin Girmamawa
Tsohon Ministan Ilimi na Najeriya, Malam Adamu Adamu, CON, na shirin samun digirin girmamawa daga Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Tarayya da ke Azare, Jihar Bauchi.
Ana sa ran jami’ar za ta ba shi digirin na girmamawa a ranar Asabar, 17 ga Oktoba, 2026, a yayin bikin yaye ɗalibanta.
Malam Adamu, wanda ke riƙe da sarautar gargajiya ta Katukan Katagum, zai samu karramawar ne bisa gudummawar da ya bayar a fannonin aikin jarida, ilimi da hidimar ƙasa.
Kafin ya shiga gwamnati, Malam Adamu ya yi fice a aikin jarida, inda ya yi aiki da jaridar New Nigerian da mujallar Citizen a Kaduna.
A lokacin aikinsa na jarida, ya shahara wajen rubuce-rubuce masu zurfin nazari, sharhin al’amuran yau da kullum da kuma amfani da hikimar magana da habaici wajen isar da saƙonni ga al’umma.
Daga baya, ya zama Ministan Ilimi a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, inda ya riƙe muƙamin daga shekarar 2015 zuwa 2023.
A lokacin mulkinsa, ya yi aiki a wani muhimmin ɓangare da ke fuskantar ƙalubale daban-daban, ciki har da samar da ingantaccen ilimi, kayayyakin more rayuwa a makarantu da kuma inganta harkokin koyarwa da koyo.
Ana sa ran bikin karramawar zai haɗa malamai, jami’an gwamnati, tsofaffin abokan aikinsa da sauran manyan baƙi domin taya shi murnar wannan nasara.
Bisa bayanan da aka bayar, an tsara fara babban bikin da ƙarfe 9:30 na safe, yayin da za a gudanar da liyafar baƙi a Kwalejin Ilimi ta Aminu Saleh da ke Azare bayan kammala bikin.
Karramawar na nuna irin gudummawar da Malam Adamu Adamu ya bayar a aikin jarida, ilimi da hidimar ƙasa.
