Connect with us

News

Amurka Za Ta Janye Sojoji 200 Daga Najeriya

Published

on

FB IMG 1787908835619

Ƙasar Amurka na shirin janye kusan sojoji 200 da ta tura Najeriya a wannan shekara domin taimakawa wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.

Rahoton jaridar The New York Times ya ce jami’an Amurka da na Najeriya sun bayyana cewa tura ƙananan rundunonin sojojin ya haifar da gagarumar nasara wajen yaƙi da mayakan ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna

Rahoton ya ce ana sa ran babban ɓangaren sojojin zai bar Najeriya zuwa ƙarshen watan Satumba, yayin da wasu ƙananan ƙungiyoyin jami’an horarwa da masu nazarin bayanan sirri za su ci gaba da kasancewa a ƙasar.

A watan da ya gabata, Kwamandan Rundunar Amurka mai kula da Afirka (AFRICOM), Janar Dagvin Anderson, ya ce Amurka ta rage yawan sojojinta a Najeriya bayan wani samame da aka gudanar a watan Mayu, wanda ya kashe Abu-Bilal al-Minuki, wanda ake zargi da kasancewa mataimakin shugaban ISIS a yankin Tafkin Chadi.

Anderson ya ce samamen ya raunana shugabancin ISIS sosai a Najeriya da ma sauran sassan duniya, yayin da ya bayyana cewa Najeriya na ci gaba da aiki tukuru wajen hana ’yan ta’adda dogaro da kansu wajen gudanar da ayyukansu.

Advertisement

Ya ƙara da cewa duk da janyewar sojojin, Amurka za ta ci gaba da haɗin gwiwar musayar bayanan sirri da Najeriya.

Wannan mataki ya zo ne makonni kaɗan bayan Najeriya da Amurka sun gudanar da zagaye na biyu na tattaunawa a Washington, ƙarƙashin wani kwamiti na haɗin gwiwa da aka kafa domin tattauna tsaron al’ummomin Kirista a yankin Arewa ta Tsakiya.

Sai dai matsalar tsaro na ci gaba da addabar wasu sassan Najeriya, inda ake fuskantar barazanar ta’addanci, ’yan bindiga, Boko Haram da ISWAP, rikicin manoma da makiyaya, da kuma ayyukan ƙungiyoyin asiri da ’yan daba.

Masana sun ce yawan rikice-rikicen tsaro a Najeriya ba ya da alaƙa da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayin Islama kaɗai, lamarin da ya sa matsalar tsaron ƙasar ke da matuƙar sarkakiya.

 

THE CABLE 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending