Sports
Osasuna ta lallasa Barcelona da ci 4 da 2
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar kwallon kafa ta Osasuna Ta yi Kalaci Tare da Daka wawa akan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da Ci 4 da Biyu a cigaba da Karawa a gasar Laliga ta kasar Sifaniya.
Kungiyar ta Osasuna ta saka Barcelona a Kwana inda ra rinka Tafka tamkar ta samu nama,kafin Barcelona ta Fara farfadowa ta farke Ci 2 daga cikin 4 da Osasuna ta nana mata.
Ƙungiyoyin Fararen Hula Za Su Sake Fita Zanga Zangar Tsadar Rayuwa A Najeriya
Wannan ne karo na Farko da Barcelona ta sha kashi tun fara Gasar Laliga ta bana,wanda wannan Ya sanya Alkadarinta ya karye na Buga wasa ba tare da an ci Nasara akanta ba a gasar ta Laliga.