News
Ƙungiyoyin Fararen Hula Za Su Sake Fita Zanga Zangar Tsadar Rayuwa A Najeriya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ƙungiyoyin da kiraye-kirayen sake fita zanga zangar adawa da manufofin gwamnati da suka haddasa matsi da tsadar rayuwa ga al’ummar Najeriya.
Duk da yadda zanga-zanga da ta gudana a baya ta juye zuwa tarzoma tare da haddasa asarar ɗimbin rayuka musamman a jihohin arewacin Najeriya.
Tsadar Rayuwa: Har Yanzu Ba A Haifi Masu Ceto Najeriya Daga Halin Ni Ƴa Su Ba – Jigo A Jam’iyyar APC
Kungiyoyin yayin wani taronsu a jihar Lagos ta yankin kudanci, sun ce wajibi ne fita zanga zangar a ranar 1 ga watan gobe na Oktoba wato ranar da ƙasar za ta bikin tunawa da ranar samun ƴanci kamar yanda FRI ta ruwaito
A cewar ƙungiyoyin za su ci gaba da dawa da manufofin gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu da suka ƙunshi janye tallafin man fetur tsaurara manufofin kuɗi da kuma hauhawar farashin kayaki.
Yayayin zanga-zanga watan jiya wadda aka yi wa laƙabi da #EndbadGovernanceinNigeria, an ga fitar dubban mutane a manyan biranen Najeriya, inda Amnesty International ke cewa mutane 21 suka mutu yayinda rundunar ƴan sandan ƙasar ta ce mutum 7 kaɗai suka mutu kuma jami’an tsaron ƙasar basu da hannu a kisan ko da mutum guda.
Masu zanga-zangar dai na neman lallai gwamnatin ƙasar ta rage farashin man fetur da na abinci baya ga lantarki da kuma sakin ilahirin masu zanga-zangar da aka kame a baya.
