Connect with us

News

Zaki Ya Kashe Ɗaya Daga Cikin Masu Kula Da Shi Aa Gonar Obasanjo

Published

on

Zaki Ya Kashe Ɗaya Daga Cikin Masu Kula Da Shi Aa Gonar Obasanjo

 

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Advertisement

Ana fargabar cewa wani Zaki ya yi Sanadiyyar mutuwar  ɗaya daga cikin masu kula da shi a cibiyar ajiye namun dawa ta tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da ke birnin Abeokuta a Jihar Ogun.

Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar Asabar, in

Advertisement

Osasuna ta lallasa Barcelona da ci 4 da 2

da Zakin ya yi wasan kura da mutumin, Babaji Daule mai shekaru 35 wanda a dalilin haka ya ce ga garinku nan.

Kakakin ’yan sandan Jihar Ogun, Omolola Odutola, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa babban jami’in tsaro a Gandun Adana Namun Dawar na Obasanjo ya sanar da su.

Advertisement

Sai dai kakakin ’yan sandan ya ce tsautsayi da ba ya wuce ranarsa ne ya sanya mutumin da lamarin ya rutsa da shi ya yi sakacin barin sakatar da ke killace Zakin a cikin keji bayan ya bai wa namun dawar abinci.

Ya ce wannan lamari ne ya bai wa Zakin damar fitowa kuma ya far wa mai kula da shi, inda ya ji masa rauni a wuya kuma a dalilin haka ajali ya katse masa hanzari.

Advertisement

Ya ƙara da cewa, an ajiye da gawar mutumin a ɗakin killace gawarwaki da ke Babban Asibitin Ijaye.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending