News
NSCDC Ta Kori Jami’inta Da Ake Zargi Da Hada Baki Da ‘Yan Bindiga A Zamfara
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar tsaro na Sibul Difens (NSCDC), reshen jihar Zamfara, ta kori wani jami’in ta, Maikano Sarkin-Tasha, bisa zargin hada baki da ‘yan bindiga wajen samar musu da muggan kwayoyi da harsasai.
Kwamandan rundunar, Sani Mustapha ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin da yake ganawa da manema labarai a Gusau.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara a ranar Juma’a ta gabatar da wasu mutane 17 da ake zargi da hada baki da ‘yan bindiga ciki har da Sarkin-Tasha.
Mustapha ya ce rundunar ba ta ji daɗin samun labarin damke jami’in ta da ake zargi da hannu dumu-dumu wajen mu’amula da ƴan bindiga ba.
“A bisa bincikenmu na farko, an kama jami’in ne a wani shingen bincike, tsakanin Damba da Sabon Gida, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa kauyen Mada da ke karamar hukumar Gusau.
“An same shi da wasu abubuwa da ake zargin wiwi ne da wasu muggan kwayoyi.
“Sauran kayayyakin da aka samu a jikin sa sun hada da sulke guda uku na G3 da sulke guda daya na harba roka.
Mustapha ya ce wannan ba ɗabi’a ba ce ta jami’an rundunar a Zamfara. Daga nan sai ya kara da cewa rundunar za ta ci gaba da saka ɗa’a da kishin kasa a zukatan jami’anta.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
