News
Satar Kuɗin Al’umma Da Masu Riƙe Da Muƙamai Ke Yi Shi Ne Babban Ƙalubalen Da Ke Gurgunta Najeriya —Sanata Ndume
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa satar kuɗin al’umma da masu riƙe da muƙamai ke yi shi ne babban ƙalubalen da ke gurgunta Najeriya.
Ndume ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Kano, a ranar Asabar.
NSCDC Ta Kori Jami’inta Da Ake Zargi Da Hada Baki Da ‘Yan Bindiga A Zamfara
“Babban ƙalubalen da ke addabar ƙasar nan shi ne cin hanci da rashawa. Har yau babu wata nagartacciyar dokar da za ta iya magance satar kuɗaɗe da ‘yan siyasa ke yi a ƙasar nan.
“Idan ka samu mutumin da ba ya satar kuɗaɗe a cikin ‘yan siyasa ko cikin gwamnati, to wannan mutumin ya yi sa’a, ya na da tsoron Allah.
“Amma dai kam, a Najeriya ce kaɗai za ka saci maƙudan kuɗaɗe, ka riƙa yawo ka na hura hanci. Su kuma jama’a su riƙa alfahari da kai.
“Idan ka zo a wuri kamar nan, mutane za su riƙa ba ka girma, su na kwantawa su na gaishe, duk fa da cewa sun sa kai ƙasurgumin ɓarawo ne.
“A Najeriya ce kaɗai wanda ba shi da ko sisi jiya ko shekaranjiya, washegari kuma ka ga ya sayi motocin hawa 10, ya sayi jiragen sa na shawagi, kuma ka ga iyalan sa su na murna da ‘nasibin’ da ya samu,” inji Ndume.
Ya ce ya yi fafutikar ganin a majalisa an kafa dokar tilasta sani yadda mutum ya kuɗance a lokaci ɗaya, amma abin baƙin ciki, har yau bai samu goyon bayan da za a yi nasarar kafa dokar ba.
