Connect with us

News

Zanga Zanga: Firaministar Bangladesh Sheikh Hasina Ta Sauka Daga Mulki Tare Da Tserewa Daga Babban Birnin Kasar

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Firaministar Bangladesh Sheikh Hasina ta sauka daga muƙaminta, a cewar babban hafsan sojin ƙasar, yana mai cewa gwamnatin riƙon ƙwarya za ta jagoranci ƙasar har lokacin da za a yi zaɓe.

Sai dai ba a san inda take ba ko da yake rahotanni na cewa ta tsere daga ƙasar bayan masu zanga-zanga sun kutsa kai cikin gidanta.

DSS Ta Kama Jagoran Zanga-zangar Yunwa Micheal Lenin A Abuja

Babban hafsan sojojin ƙasar Waker-Uz-Zaman ya roƙi masu zanga-zangar su koma gida domin ƙyale sojoji mu maoido da zaman lafiya.

Advertisement

Wannan mataki ya kawo ƙarshen shekara 15 na jam’iyyar Awami League, wadda ita ce jam’iyyar mutumin daya kafa ƙasar.

Tun da farko rahotanni sun ce Hasina tare da ‘yar’uwarta, sun fice daga Dhaka a yayin da zanga-zanga ta yi ƙamari.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *