News
DSS Ta Kama Jagoran Zanga-zangar Yunwa Micheal Lenin A Abuja
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar ƴan sandan farin kaya sun kama ɗaya daga cikin jagororin zanga-zangar yunwa a Abuja, Micheal Lenin.
Jaridar Blueprint ta ruwaito cewa hakan ya faru ne karfe biyu na safiyar ranar litinin, inda suka ɗauke shi a gidan shi da ke unguwar Apo a cikin babban birnin tarayya Abuja.
Daraktan “Take it back movement” Damilare Adenola, ya tabbatar da faruwan haka, kuma ya ƙara da cewa jami’an sun ci zarafin Micheal a gaban iyalansa kafin su tafi dashi.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, an kasa samun kakakin rundunar ƴan sandan farin kaya,
Peter Afunaya a wayar salula. Kuma bai maido amsar saƙonni da aka tura ma shi ba.
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News2 days ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News7 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
