Connect with us

News

Mata 7 Sun Rasa Ransu Yayin Da Wasu Suka Samu Raunuka A Lokacin Wata Zanga-zanga A Adamawa

Published

on

Women protesting over killings in Adamawa communities

Akalla mata bakwai suka rasa rayukansu, yayin da wasu goma sha ɗaya suka samu raunuka a lokacin wata zanga-zanga da aka gudanar a jiya a ƙaramar hukumar Lamurde ta jihar Adamawa, a shiyar Arewa maso gabashin Najeriya.

Rahotanni daga jaridar Daily Trust sun nuna cewa matan, wadanda ke riƙe da ganyayyaki, sun gudanar da zanga-zangar ne domin nuna rashin jin daɗinsu kan jinkirin isowar sojoji wajen kwantar da tarzomar da ta ɓarke tsakanin ƙabilar Bachama da Chobo a yankin.

Advertisement

Gwamnan Jihar Osun Adeleke Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam’iyyar Accord

A cewar wasu majiyoyi, yayin da ake ta tattaunawa tsakanin sojojin da matan masu zanga-zangar, jami’an sojin sun yi harbi cikin dandazon masu zanga-zangar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mata huɗu nan take, sannan wasu uku suka mutu a asibiti. Haka kuma wasu mutum goma sha ɗaya suka ji rauni.

Hakimin Gyawana na ƙaramar hukumar Lamurde, Agoso Bamaiyi, ya tabbatar da cewa waɗanda suka samu raunuka suna kwance a babban asibitin Numan, inda jami’an lafiya suka bayyana cewa wasu na cikin mawuyacin hali.

Advertisement

Bayan faruwar lamarin, Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a yankin Lamurde, tare da umurnin gaggauta maido da zaman lafiya ta hanyar jami’an tsaro.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending