News
Jihohi 7 Za Su Fuskanci Katsewar Wutar Lantarki Na Tsawon makonni A Arewacin Najeriya
Masu amfani da wutar lantarki a jihohi bakwai — Filato, Gombe, Bauchi, Borno, Adamawa, Taraba da Yobe — za su fuskanci katsewar wuta na tsawon makonni sakamakon shirye-shiryen katse wuta a layin wutar lantarki na Jos–Gombe mai ƙarfin 330kV.
Hukumar dake Kula da Tsarin Wutar Lantarki ta Nijeriya ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, inda ta ce katsewar za ta gudana daga ranar 9 ga Afrilu zuwa 22 ga Mayu, 2026.
Amurka Ta Bai Wa Jami’anta Umarnin Barin Ofishin Jakadancinta Na Nijeriya
A cewar hukumar, katsewar wutar za a rika yinta ne duk mako daga ranar Alhamis zuwa Lahadi, daga ƙarfe 9:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.
Ta bayyana cewa an shirya katse wutar ne domin samar da damar girka kayan sadarwa na ‘fibre optic’ na karkashin kasa a kan layin wutar, a wani bangare na kokarin inganta tsarin wutar lantarki ta kasa.
“Hukumar Kula da Tsarin Wutar Lantarki ta Nijeriya na sanar da masu amfani da wutar a jihohin da abin ya shafa cewa za a katse wuta a layin Jos–Gombe 330kV daga ranar 9 ga Afrilu zuwa 22 ga Mayu, 2026.
“Wannan katsewar ya zama dole domin samar da damar girka kayan fibre optic na Optical Ground Wire a kan layin,” in ji sanarwar.
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
