Connect with us

News

‎KANO: Hatsarin Kwale-kwale Ya Yi Ajalin Mutum A Bagwai ‎

Published

on

FB IMG 1723570815626

Wani hatsarin kwale-kwale da ya biyo bayan tasowar iska mai ƙarfi ya yi sanadin mutuwar mutum guda, yayin da wasu biyu suka tsira da raunuka a Dam ɗin Bagwai da ke Ƙaramar Hukumar Bagwai a Jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar Talata, lokacin da wata guguwa ta taso ba zato, lamarin da ya kifar da kwale-kwalen da ke ɗauke da mutane uku.

Advertisement

Jihohi 7 Za Su Fuskanci Katsewar Wutar Lantarki Na Tsawon makonni A Arewacin Najeriya 

The stentor news ta ruwaito cewa mutanen na kan hanyarsu ne daga Ƙaramar Hukumar Tsanyawa zuwa Bagwai domin kai ziyara ga wani ɗan uwansu da ke jinya a asibiti, lokacin da hatsarin ya rutsa da su.

Advertisement

‎Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Sarkin Ruwa na Bagwai, Malam Murtala Umar, ya ce masunta sun yi gaggawar kai dauki domin ceto waɗanda abin ya shafa. Ya ce an ceto Aliyu mai shekaru 25 da Dan’garba mai shekaru 45 da ransu, duk da cewa sun samu raunuka, yayin da Saminu mai shekaru 35 ya rasu a wurin.

‎Wani daga cikin masu aikin ceton, Malam Aminu Adamu Liringo, ya danganta hatsarin da tsananin iska da ta haddasa mummunan motsin ruwa wanda ya jawo kifewar kwale-kwalen.

Advertisement

‎A nasa bangaren, Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Masunta, Malam Inusa Aliyu, ya bukaci hukumomi da su dauki matakan inganta tsaron sufuri a ruwa, ciki har da samar da ingantattun kwale-kwale da kuma ƙarfafa hanyoyin agajin gaggawa.

‎Shi ma Shugaban Ƙaramar Hukumar Bagwai, Alhaji Bello Abdullahi Gadanya, ya bayyana alhinin sa kan faruwar lamarin, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan mamacin.

Advertisement

‎Ya ƙara da cewa hukumomi na kokarin ɗaukar matakan da suka dace domin hana aukuwar irin wannan hatsari a nan gaba, ciki har da inganta tsaro a harkokin sufuri ta ruwa.

‎A cewar jami’in yaɗa labarai na yankin, Shehu Bello Shanono, an ceto mutum biyu a ranar da hatsarin ya faru, yayin da aka gano gawar mamacin a washegari.

Advertisement

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending