Connect with us

News

Sakacin Gwamnati Ne Ke Haifar Da Mutuwar Dubban Mutane Saboda Haɗarin Jiragen Ruwa A Najeriya —PREMIUM TIMES

Published

on

kwale kwale

 

Kamar sauran hanyoyin sufuri na Najeriya, hanyoyin zirga-zirga ta ruwa sun zama tarkon da ke cin rayukan al’umma, musamman ga masu amfani da kwale-kwale domin tsallake ruwa wanda ke cigaba da haifar da asarar rayuka masu yawan gaske.

Advertisement

Yawan faruwar ibtila’in haɗarin jirgin ruwa abu ne da ke nuna gazawar mahukuntan na ɗaukar matakin da ya kamata domin tsare rayuwa da lafiyar al’ummar da nauyi ya rataya a wuyansu.

Ƙarin Farashin Litar Man Fetur Ya Tilastawa Kanawa Yin Tafiyar Ƙafa

Ya kamata – la’akarin da faruwar irin wannan ibtila’in da aka samu a kusan jihohi 10 na ƙasar nan – mahukunta su sauya tunani da salonsu daga jajanta wa iyalan waɗanda suka gamu da wannan ibtila’in da shugaban ƙasa da gwamnoni ke yi zuwa ga ƙoƙarin ɗaukar matakan da suka kamata domin ganin kawo ƙarshen matsalar.

Advertisement

Ibtila’i na baya-bayan nan shi ne wanda ya faru a jihar Legas, inda wasu jiragen ruwa suka yi taho-mu-gama a ranar Litinin wanda ake zargin ya haifar da rasa rayukan mutane 21. Domin bisa rahotanni sun nuna cewa akwai mutane 16 a cikin kowanne jirgi a yayin da wannan haɗari ya faru da daddare a ƙaramar hukumar Amuwo-Odofin da ke jihar.

 

Advertisement

Bai kamata a riƙa samun irin wannan ibtila’in yana faruwa ba, idan har hukumomin da abin ya shafa a matakan jigohi da gwamnatin tarayya suna sauke nauyin da ya rataya a kansu.

 

Advertisement

Abu ne da ya saɓa doka tuƙa jirgin ruwa idan ya wuce tsakankanin ƙarfe 6 na safe zuwa 6na yamma a cewar Hukumar Sufurin Ruwa ta Ƙasa wanda Ma’aikatar Shari’a ta tabbatar.

 

Advertisement

Kafin wannan ibtila’i na jihar Legas, an samu irin makamancin irin waɗannan haɗura.

 

Advertisement

A ranar 3 ga watan Oktoba, an samu haɗari da ya rutsa da fasinjoji 300 waɗanda suka haɗa da mata da ƙananan yara kuma dukkanninsu sun nutse.

 

Advertisement

Wannan al’amari ya faru ne a yayin da suke dawowa daga biki daga ƙaramar hukumar Mokwa a jihar Neja.

 

Advertisement

Mutane 160 ne aka iya cetowa, inda aka samu rahotanni na mutuwar mutane 60 da suka rasa rayukansu, sannan an nemi kusan mutane 108 ba a gan su ba.

 

Advertisement

Haka ma a jihar Zamfara inda mutane 40 suka mutu a irin makamancin wannan haɗari a watan Satumba a ruwan da ake kira da Bakin Kasuwa da ke ƙaramar hukumar Gumm. A watan Agusta kuwa, an samu fashewar wani jirgin ruwa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 20 a Ezetu 1 da ke Kudancin Ijaw.

 

Advertisement

Haka ma wasu fasinjoji 250 sun gamu da haɗari a hanyar ruwa ta Buguma a ƙaramar hukumar Asari-Toru a jihar Ribas a yayin da suke dakon kaya a watan Afirilu, sai dai sun yi sa’a ba wanda ya rasa rainsa bayan ɗauki da rundunar sojin ruwa ta ƙasa ta kai musu.

 

Advertisement

Jirgin ruwan nasu dai haɗin gida mai hawa uku wanda rundunar ta ce an yi masa lodin da ya fi ƙarfinsa ne kuma babu wanda ke sanye da rigar kariya a cikinsu.

 

Advertisement

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ya kamata ta tabbatar da kare rayukan masu amfani da jiragen ruwa manya da ƙanana, musamman tabbatar da dokar da ba a bi ta yin zirga-zirga tsakanin ƙarfe 6 na safe zuwa 6 na yamma da kula da yawan kayan da za a ɗora wa jiragen ruwan kafin tashinsu da kuma safaya na sandunan tura jiragen domin ko-ta-kwana a lokacin da injin wani jirgi ya mutu; waɗanda dokoki ne ga masu jiragen da kuma matuƙan jiragen.

 

Advertisement

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa a shekarar 2022, bayan la’akari da yadda ake karya waɗannan ƙa’idoji da kuma umarnin ma’aikatar shari’a ta ƙasa, ta ɗau aniyar ganin ta tabbatar da an riƙa bin matakan tare da bayyana cewa duk wanda aka samu da karya dokokin tun zai yi zaman gidan kaso na shekaru 7. Sai dai wannan mataki ya zama ihunka banza domin kuwa hukumar ba ta cika wannan alwashi da ta ɗauka ba.

 

Advertisement

Baya ga ɗabi’ar nan ta ɗaukar kayan da suka wuce gona da iri, jirage da yawa sun sha fashewa saboda dukan duwatsu saboda hanyoyinmu na ruwa ba a cika yashe su ba yadda ya kamata. Akwai buƙatar a kula da hanyoyin ruwa masu tsayin kilomita 10,000 da muke da su a wannan ƙasa.

 

Advertisement

Don haka, kamata ya yi a ɗora wa Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa laifin faruwar waɗannan haɗura da kuma Ma’aikatar Sufuri ta Ƙasa waɗanda ya kamata su haɗa kai wajen tabbatar da tsaron rayukan mutanen da rayuwarsu ta ta’allaƙa da amfani da hanyoyi na ruwa.

 

Advertisement

Wani bincike da Premium Times ta gudanar da haɗin guiwar Pluboard wanda aka fara shi a 2019 zuwa 2023, ya nuna an samu mutuwar aƙalla mutane 1072 daga haɗura 71 da aka samu. An samu mutane 106 da suka mutu a jihar Kwara a watan Yunin 2023 da mutane 100 a jihar Taraba a watan Oktoba a 2023. Haka kuma an samu mutuwar mutane a 98 a jihar Kebbi a 2021da sauran jihohi kamar Anambra, Kano, Sokoto, Kuros Ribas, Neja da sauransu.

 

Advertisement

A yayin taron wayar da kai game da amfani da hanyoyin sufuri na ruwa 2024, Manajin Daraktan Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa, Bola Oyebamiji, ya bayyana rashin ilimi da sakaci da ƙin bin ƙa’ida a matsayin a abubuwan da ke haifar da wannan matsala. Inda ya tabbatar da cewa lokaci ya yi da za a tilasta wa mutane bin waɗannan ƙa’idoji.

 

Advertisement

Ya ba da misali da cewa a ƙasar Ingila, sai mutum ya samu takardar shaidar sahalewar hukuma kafin ya fara amfani da hanyoyin ruwa kuma ana bibiyar masu wannan shaida a duk bayan shekaru huɗu kuma an ƙayyade cewa ka da gudun kowanne irin abin hawa na ruwa ya wuce mil huɗu a awa ɗaya.

Don haka, akwai buƙatar hukumar ta sanya jami’anta a kowanne wuri da ake sufurin jiragen ruwa domin tabbatar da an bi dokar matakan kariya.

Advertisement

 

Sannan muna ba wa gwamnati shawar yin rajistar matuƙa jirgin ruwa a kowanne gari domin tabbatar da bin waɗancan dokoki wana zai taimaka wajen rage mace-macen mutane.

Advertisement

 

Da yawan waɗanda kan gamu da irin wannan ibtila’i dai manoma ne da ‘yan kasuwa waɗanda ke kawo kayan abincinsu zuwa kasuwannin birane. Kuma waɗannan muhimman abubuwa ne da ke bunƙasa tattalin arziƙin a yayin da ƙasar ke fuskantar matsalar ƙarancin abinci da tsadarsa. Don haka, Najeriya ce ke yin asara idan aka samu irin waɗannan haɗura.

Advertisement

 

Saboda haka, kamar yadda ake ƙoƙarin kare rayukan masu kuɗin da ke amfani da jiragen sama ta hanyar kula da dokoki masu tsanani, duk da ba a ma cika kula da ƙa’idojin tuƙi na kan tudu (hanyoyin motoci) ba, su ma dai mutanen da ke amfani da hanyoyi na ruwa suna da buƙatar makamanciyar irin wannan kulawa.

Advertisement

 

Akwai buƙatar Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta ƙasa da kuma waɗanda ke yankunan ƙasar nan su tabbatar da al’umma cewa akwai su kuma suna aikin da ya kamata wajen kula da hanyoyin ruwa da muke da su a Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending