Connect with us

News

Ƙarin Farashin Litar Man Fetur Ya Tilastawa Kanawa Yin Tafiyar Ƙafa

Published

on

Yadda Ƙarin farashin man fetur ke tilasta Kanawa yin tafiyar ƙafa

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Ƙarin farashin man fetur da aka yi ƙara jawo guna-guni a wajan fasinjoji yayin da direbobi ke cewa da ma can ba wata ribar kirki suke samu ba jihar Kano.

Tun kafin ƙara farashin a yanzu mazauna jihar Kano kan sayi litar mai kan sama da N1,000.

Wani Bene Mai Hawa 2 Ya Ruguje A Legas

Amma a yanzu masu ababen hawa kan ce akan samu man Fetur din a NNPCL kan N1,070, yayin da ‘yan kasuwa kan sayar a N1,050 zuwa 1150 zuwa N1,250.

Wata ɗaliba ta bayyana cewa N1,500 bai zama lallai su kai ta inda za ta je ba kuma ta riga ta fito titi.

“Daga Unguwar Uku na ke zuwa Yusuf Maitama University da ke Kabuga kuma Naira 800 ba zaka kaini makaranta ba ni ɗaliba ce,” a cewar ɗalibar da ba ta bayyana sunanta ba.

Advertisement

Wani ɗankasuwa ya ce tsadar kuɗin Adaidaita sahu ya sa yake tafiyar kusan N100 a ƙafa kullum idan zani kasuwa.

“Ina kashe N1,200 daga gidana zuwa kasuwa, ,” kamar yadda ya baiyyana wa Jaridar INDA RANKA

Haka zalika wani dalibin Jami’ar Bayero dake Kano dake Karantar fanninn sadarwa mai suna jawahir Adam yace a baya yana kashe Naira 400 kacal idan zashi makaranta amman Kuma yanzu yana kashe sama da Naira 700 bayan tafiyar kasan da yakeyi domin ya Kara samun saukin kudin Mota.

“Gaskiya an shiga wani hali na takura, ya kamata shugabanninmu su duba halin da talakawa ke ciki, su nema mana sassauci,” a cewarsa.

Bisa al’ada, kuɗin zirga-zirga na ƙaruwa nan take da zarar an ƙara farashin fetur ɗin, kuma a wannan karon direbobi ma sun koka cewa lamarin ya shafe su sosai.

Wani Direban Babbar Mota ya bayyanawa Jaridar Inda Ranka cewa a baya duk da Janye tallafin Mai suna samin fasinjiji akai akai amman yanzu tsadar mai tayi kamari.

Advertisement

Ya Kara da cewa a yanzu basa samun fasinjojin da yakamata dalilin tsadar mai gashi kuma sunada Iyali ga kudin balance.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending