Connect with us

News

Ƴan Bindiga Sun Harbi Babban Kwamandan Dakarun Sa Kai Na Zamfara

Published

on

AFGHANISTAN UNREST TALIBAN

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

A Wata musayar wuta da aka yi a tsakanin ƴan bindiga da dakarun tsaro na sakai CPG a jihar Zamfara

Advertisement

PRNIGERIAN ta ruwaito cewa Ƴan bindiga sun kashe mutane dama inda suka raunata wasu cki har da babban kwamandan rundunar ƴan sa kan Janar Lawal B. Muhammad mai ritaya.

Sakacin Gwamnati Ne Ke Haifar Da Mutuwar Dubban Mutane Saboda Haɗarin Jiragen Ruwa A Najeriya —PREMIUM TIMES

Rahotanni dai sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun tare hanyar Funtua zuwa Tsafe ne mai cike da cunkoson jama’a da yammacin ranar lahadi, inda suka far wa masu ababen hawa ciki har da Darakta janar na hukumar ta CPG.

Advertisement

Sannan a yayin wannan samamen ƴan bindigar sun yi awun gaba da wasu fasinjoji da dama dake kan hanyarsu ta zuwa wurare daban-daban.

Wata majiya daga ma’aikatar tsaron cikin gida ta jihar Zamfara, wadda ta bukaci a sakaya sunanta, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma ce shugaban na samun kulawa a wani asibiti da ke Gusau, babban birnin jihar.

Advertisement

Wannan arin na zuwa ne kwanaki kadan bayan da ‘yan bindiga suka kashe jami’an na CPG akalla takwas da wani direban motar sufuri a karamar hukumar Tsafe da ke jihar ta Zamfara.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi wa jami’an na CPG kwanton bauna ne kafin su an kara suka bude musu wuta.

Advertisement

Da yake bayani game da harin, babban kwamandan da aka harba ya bayyana cewa, bayan da ya fahimci cewa ‘yan bindigar na shirin kai hari a tsafe, sai ya tura jami’an CPG 105 zuwa karamar hukumar tare da ajiye su a wannan wuri domin baiwa matafiya kariya ba tare da sanin sun musu riga Malam masallaci ba.

Sai gashi abin bakin ciki ƴan bindigar sukai musu kwanton bauna saboda sun kwana a wurin, a yayin da dakarun sa kan suke sauka sai suka bude musu wuta kuma suka kashe wasu daga cikinsu tare da jikkata wasu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending