News
Kifewar Kwale-kwale Ta Yi Ajalin Manoma Biyar A Neja
Akalla manoma biyar, maza huɗu da mace ɗaya, sun rasu bayan wani kwale-kwale da suke ciki ya kife a Kogin Kudi, da ke Ƙaramar Hukumar Katcha ta Jihar Neja.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a ƙauyen Shaba-Woshi-Kpaya, da ke gundumar Edotsu, lokacin da manoman ke kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu.
Jami’an NDLEA Sun Cafke Miyagun Kwayoyi Da Darajarsu Ta Haura Biliyan 3
Wani mazaunin yankin, Muhammadu Dan-Asabe, ya shaida wa Daily Trust cewa manoman suna tafiya ne daga ƙauyensu zuwa gonakinsu ta hanyar ruwa a lokacin da kwale-kwalen ya kife.
Daraktan Yaɗa Labarai da Ayyuka na Musamman na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Dr Ibrahim Audu Hussaini, ya tabbatar da faruwar hatsarin.
Hussaini ya ce waɗanda abin ya rutsa da su suna kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu ne lokacin da kwale-kwalen ya kife.
Ya bayyana cewa an gano gawawwakin mutanen biyar, sannan aka yi musu jana’iza a ranar Asabar.
An bayyana sunayen waɗanda suka rasun da Yahaya Abubakar, Usman Abubakar, Lami Hussaini, Baba Ahmadu da Salihu Aliyu.
Hadarin kwale-kwale ya zama ruwan dare a wasu al’ummomin da ke zaune a bakin koguna a Nijeriya, musamman a lokacin damina, lokacin da manoma ke yawan amfani da hanyoyin ruwa wajen zirga-zirga zuwa gonakinsu.
Lamarin ya sake jaddada buƙatar ƙara matakan tsaro da wayar da kan mazauna yankunan da ke dogaro da hanyoyin ruwa, musamman wajen amfani da kwale-kwale a lokacin damina.
