News
Akwai Yiwuwar Ballewar Dam Ɗin Challawa — Gwamnatin Tarayya
Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are ta gargadi mazauna yankunan da ke kusa da kogin Challawa Kano zuwa Hadejia da su yi taka-tsantsan, sakamakon karuwar ruwan sama da ake samu a wasu sassan yankin.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce ana sa ran ƙarin ruwan sama zai iya ƙara yawan ruwan da ke kwarara zuwa madatsun ruwa na Challawa da Tiga, lamarin da ka iya sa madatsun su kai matsayin cika.
Ambaliyar Ruwa Ta Shanye Hanyoyi, Ta Jefa Masu Ababen Hawa Cikin Mawuyacin Hali A Abuja
Hukumar ta bayyana cewa idan ruwan ya ƙaru sosai, akwai yiwuwar samun ƙarin kwararar ruwa a kogin Kano–Hadejia, wanda hakan ka iya haifar da ambaliya a wasu al’ummomin da ke zaune a kusa da kogin.
Saboda haka, ta buƙaci mazauna yankunan da kogin Kano–Hadejia ya ratsa su kasance cikin shirin ko-ta-kwana tare da sanya ido kan yanayin ƙaruwar ruwa.
Hukumar ta kuma shawarci jama’a da su bi umarnin hukumomin da abin ya shafa tare da ɗaukar matakan kariya domin kare rayukansu da dukiyoyinsu daga illar ambaliyar ruwa.
Haka kuma, ta yi kira ga hukumomin da ke da alhakin kula da yankunan da abin ya shafa da su ɗauki matakan gaggawa domin rage haɗarin ambaliya da kuma kare al’ummomin da ke bakin kogin.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da sanya ido kan yanayin ruwan tare da sanar da jama’a duk wani sabon ci gaba da ya taso, musamman idan aka samu ƙarin haɗarin ambaliya ko cikar madatsun ruwan.
