News
Ambaliyar Ruwa Ta Shanye Hanyoyi, Ta Jefa Masu Ababen Hawa Cikin Mawuyacin Hali A Abuja
Ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na Abuja a ranar Asabar, lamarin da ya kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa tare da tilasta wa wasu ‘yan kasuwa rufe wuraren kasuwancinsu.
Ambaliyar ta shafi wurare da dama, ciki har da Adetokunbo Ademola Crescent da ke Wuse 2, yankin da ke kusa da Delight Event Centre a Gudu, da wasu sassan Efab Estate da ke Lokogoma.
Jama’a Sun Yi Cirko-Cirko Domin Dibar Ganimar Man Da Tankar Mai Ta Zubar
Gadar da ta haɗa Gaduwa da Durumi ita ma ta cika da ruwa, lamarin da ya hana masu ababen hawa wucewa cikin sauƙi. Wasu motoci sun makale, yayin da wasu kuma suka samu matsala .
Wani mazaunin yankin da ya ɗauki bidiyon ambaliyar a hanyar Ebeano-Gudu ya yi kira ga Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da ya gaggauta magance matsalar.
Ya ce ambaliyar ta katse hanyar da ke haɗa Ebeano da Gudu, inda masu ababen hawa daga bangarorin biyu suka kasa wucewa, lamarin da ya tilasta musu neman wasu hanyoyi.
Lamarin ya sake haifar da tambayoyi kan ingancin matakan da ake ɗauka wajen magance ambaliyar ruwa da kuma yanayin magudanan ruwa a Abuja, musamman ganin makudan kudaden da aka ware domin magance matsalolin muhalli.
Bayanan Ofishin Akanta-Janar na Tarayya sun nuna cewa sama da Naira biliyan 109.5 daga Asusun Kula da Muhalli na Najeriya (Ecological Fund) aka fitar tsakanin Yulin 2023 da Disamban 2025 domin magance matsalolin muhalli, musamman ambaliyar ruwa.
Jimillar N109,516,046,114.35 ce aka raba wa gwamnatocin jihohi da Babban Birnin Tarayya da sauran hukumomi domin ƙarfafa matakan dakile ambaliyar ruwa, inganta magudanan ruwa da magance sauran matsalolin muhalli.
Sai dai duk da fitar da wadannan kudade, ambaliyar ruwa na ci gaba da addabar wasu sassan Abuja, tare da haddasa asarar dukiya da kuma kawo cikas ga zirga-zirgar jama’a.
Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) da Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya (NIHSA) sun yi gargadin cewa wasu sassan ƙasar na iya fuskantar ambaliyar ruwa a lokacin daminar 2026, musamman a watan Agusta da Satumba.
