Connect with us

News

Magidancin Ya Cinna Wa Matarsa Wuta Bayan Wani Saɓani Da Ya Shiga Tsakaninsu

Published

on

IMG 20260816 232250 038

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kogi ta kama wani magidanci, Jacob Irewa, bisa zargin ƙoƙarin kashe matarsa, Berida Irawo, bayan wani saɓani da ya shiga tsakaninsu a Lokoja.

Kakakin rundunar, ASP Salisu Afusat, ta ce lamarin ya faru ne ranar Juma’a, 14 ga Agusta, 2026, da misalin ƙarfe 8:30 na dare a Oworo Estate, Felele, cikin birnin Lokoja.

Ambaliyar Ruwa Ta Shanye Hanyoyi, Ta Jefa Masu Ababen Hawa Cikin Mawuyacin Hali A Abuja

Ta ce ƙungiyar sa ido ta sashen ’yan sanda na B Division da ke Felele ta samu rahoton lamarin, inda jami’an suka garzaya wurin tare da kama wanda ake zargin.

A cewar rundunar, binciken farko ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne bayan matar ta ƙona wasu daga cikin kayan mijinta da take ganin ba ya amfani da su, ba tare da izininsa ba.

Rundunar ta ce bayan faruwar hakan, Irewa ya yi wa matarsa barazana, sannan ya ɗauko fetur daga babur ɗinsa, inda ya zuba mata tare da cinna mata wuta.

Advertisement

Sai dai matar ta tsira daga harin, kuma a halin yanzu tana karɓar magani a asibitin Honey Gold da ke Felele, Lokoja.

Kakakin rundunar ta ce wanda ake zargin ya amince a bayanin da ya yi wa ’yan sanda cewa shi ne ya cinna wa matarsa wuta. Ta ce an fara gudanar da cikakken bincike domin gano ƙarin bayanai kan lamarin.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending