News
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gargadi Game Da Yiwuwar Fuskantar Ambaliyar Ruwa A Jihohi 10
Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗin cewa wasu yankuna a cikin jihohi 10 na Najeriya za su iya fuskantar ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, lamarin da zai iya janyo ambaliyar ruwa, tsakanin ranar 8 ga watan Afrilu zuwa 12 ga watan Afrilu na shekarar 2026.
Cibiyar ba da gargaɗin gaggawa game da ambaliya ta Ma’aikatar Muhalli ta Nijeriya ce ta bayar da gargaɗin a wani hasashe na ambaliya da ta fitar ranar 8 ga watan Afrilu kuma daraktan sashen kula da zaizayar ƙasa da ambaliya da kiyaye yankin gaɓar teku na ma’aikatar, Usman Bokani, ya sanya wa hannu.
KANO: Hatsarin Kwale-kwale Ya Yi Ajalin Mutum A Bagwai
“Waɗannan wuraren da kewayensu za su iya samun ruwan sama kamar da bakin ƙwarya wanda zai iya haddasa ambaliyar ruwa cikin lokacin hasashen: 8 ga watan Afrilu zuwa12 ga watan Afrilu na shekarar 2026,” in sji sanarwar.
Ma’aikatar ta ce al’ummomi a jihohin Ebonyi da Anambra da Ogun da Taraba da Cross River da Binuwe da Imo da Delta da Ribas da Abia suna cikin wuraren da za su iya samun ruwan sama kamar da bakin ƙwarya wanda zai iya haddasa ambaliya a lokacin.
