News
Sabuwar Zanga-zanga Ta Sake Barke A Adamawa Kan Zargin Kisan Mata Da Sojoji Suka Yi
Sabuwar zanga-zanga ta ɓarke a ƙaramar hukumar Numan ta Jihar Adamawa a ranar Talata, sakamakon zargin cewa wasu jami’an Sojojin Najeriya sun kashe mata yayin wani aiki na dawo da zaman lafiya a ƙaramar hukumar Lamurde da ke maƙwabtaka da ita.
Tashin hankalin ya biyo bayan rikicin ƙabilanci tsakanin al’ummomin Bachama da Chobo da ya afku a ranar Litinin.
Ɗalibi Ya Rasa Ransa A Hatsarin Mota Yayin Murnar Kammala Jarabawa A Jami’ar AAU
Majiyarmu ta ruwaito cewa mata bakwai sun mutu, yayin da 11 suka jikkata a lokacin zanga-zangar da aka yi a Lamurde, inda masu zanga-zangar suka zargi sojoji da jinkirin shiga tsakani don kwantar da tarzomar da ke tsakanin ƙabilun biyu.
An ga matan suna riƙe da ganye, suna tare hanyar shigar sojoji cikin yankin, inda suka zargi rundunar da nuna son kai ga al’ummar Chobo.
A yayin arangamar, majiyoyi sun ce sojoji su yi harbi cikin taron jama’a, inda mata huɗu suka mutu nan take, yayin da wasu mata uku suka rasu daga baya a asibiti. A halin yanzu, ana jinyar wasu da dama da suka samu raunuka a Asibitin Numan, kuma ana sa ran yawan mace-macen na iya ƙaruwa nan gaba.
Duk da cewa masu zanga-zangar sun dage cewa sojoji ne suka haddasa mutuwar, Sojojin Najeriya sun musanta hakan, suna mai cewa mutuwar ta samo asali ne daga ƴan sa-kai masu makamai da ba su da ƙwarewa wajen sarrafa bindigogi.
