Connect with us

News

Zanga Zanga:  Muna Allah Wa-Dai Da Kashe Mutane A Kurna Da Rijiyar Lemo, Da Sharaɗa A Kano —Kungiyar WAI

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Kwamared Umar Ibrahim Umar, shugaban ƙungiyar War against Injustice ya ce suna  Allah wa-dai da kashe mutane a Kurna da Rijiyar Lemo, da Sharaɗa a Kano, da sauran sassan Najeriya

Muna matukar bakin ciki da asarar rayukan da ba su ji ba ba su gani ba, da kuma amfani da karfi a kan ‘yan kasa da suke amfani da ‘yancinsu na asali da na dimokradiyya.

Advertisement

Simintin Dangote Ya Samu karuwar Kudaden Shiga A Kasuwannin Afrika

Muna kira ga rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta binciki wadannan zarge-zarge tare da daukar matakin da ya dace kan masu aikata laifin.

Muna kira ga masu ruwa da tsaki da su ba mu hadin kai wajen neman adalci ga wadanda abin ya shafa da iyalansu. Muna neman a ba da cikakken bayani kan rayukan da aka rasa da kuma jikkatar da aka samu a lokacin zanga-zangar.

Advertisement

Yin amfani da karfi kan masu zanga-zangar lumana cin zarafi ne da take hakkin bil’adama da ‘yancin walwala. Za mu ci gaba da bayar da shawarwarin kare wadannan hakkoki tare da neman a gurfanar da wadanda ke da hannu a wannan ta’asa.

Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda abin ya shafa tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending