News
Tsadar Rayuwa: Har Yanzu Ba A Haifi Masu Ceto Najeriya Daga Halin Ni Ƴa Su Ba – Jigo A Jam’iyyar APC
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Dan gani kashenin Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu kuma jigo a jam’iyyar APC, mai Mulki Joe Igbokwe, ya yi martani akan cewa har yanzu fa ba a haifo waɗanda za su cire Najeriya daga halin kunci rayuwa da take fama da shi ba.
WIKKI TIMES ta ruwaito cewa Igbokwe, daya daga cikin mutanen da suka yiwa yakin neman zaben Shugaba Tinubu tsayin daka, ya bayyana haka ne a lokacin da yake tsokaci kan yadda tsadar rayuwa ke cigaba da ta’azzara a kasar.
Likita Daya Na Kula Da MarasA Lafiya 33,000 A Kano — Ƙungiyar Likitoci
A wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook a ranar Juma’a, ya koka tare da nuna damuwa irin yadda buhun shinkafa ya yi tashin Gwauron zabi kusan Naira 100,000.
“Duk da irin kamfanonin sarrafa shinkafa da muke da su a Najeriya, sai gashi mata ta tana gaya min irin yadda buhun shinkafa ya tsefe ya kai sama da ₦100k. Saboda haka na fahimci cewa jinsin da zasu ceto Najeriya daga talauci ba a halicce su ba tukuna,” Joe ya wallafa.
Igbokwe, kasancewa an dade ana gwagwarmaya da shi tun gwamnan Legas 1999, ya fito inda aka ji yana sukar wasu daga cikin manufofin gwamnatin Tinubu,duba da irin yadda tafiyar ke chanza salo.
Makwanni biyu da suka gabata, anji ya fito ya koka kan yadda aka yi karin kudin wutar lantarki ya nemi Tinubu ya duba lamarin
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook Igbokwe ya koka da cewa wutar Naira 20,000 kwana ɗaya kawai ya yi a gidan sa.
Ya ce: “PBAT, don Allah a duba sabon kudin wutar lantarki a Najeriya. Zai kashe ‘yan kasuwa idan gwamnati ba ta hanzarta daukar mataki ba. Ina da karamin ofis a Surulere mai raka’a 7 na AC.
